Connect with us

Labarai

Da Ɗuminsa: Ƴan sanda sun hana Tashe a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta haramta yin wasan al’adar Tashe a faɗin jihar.

Rundunar ta bakin mai magana da yawun ta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Litinin.

Ya ce,”Sakamakon yadda wasu matasa ke fakewa da Tashen, suna yi wa mutane ƙwace a lokacin da su ke tsaka da wasan”.

Wannan matakin ya biyo bayan umarnin ƙwamishinan ƴan sanda CP Sama’ila Shu’aibu Dikko.

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Trending