Connect with us

Manyan Labarai

Magoya bayan Manchester United sun yi zanga-zangar lumana a Old Trafford

Published

on

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United sun gudanar da wata ‘yar karamar zanga-zangar lumana a wajen filin atisayen kungiyar a ranar Juma’a.

Kimanin magoya bayan dozin biyu ne suka taru a wajen Carrington don nuna adawa da dangin Glazer, wadanda suka mallaki kulob din.

Ana sa ran wata zanga-zanga a Old Trafford ranar Asabar kafin wasan da United za ta yi da Norwich a gasar Premier.

Uku ne kawai United ta samu nasara a wasanni 12 da ta buga a dukkanin wasanni, inda ta sha kashi a hannun Everton da ci 1-0 a ranar Asabar din da ta gabata, kuma tana da tabbacin ba za ta kai matakin karshe na bara da maki 74 ba.

‘Yan jaridun da suka isa taron manema labarai na riko na manajan Rangnick an karkatar da su zuwa wata hanya ta daban.

Wakilin wasan kwallon kafa na BBC, Simon Stone, ya ruwaito cewa magoya bayansa sun yi cudanya da masu farautar hoto yayin da da gangan suka hana zirga-zirgar ababen hawa da ke kokarin shiga harabar horo.

Sai dai Ralf Rangnick ya ce, magoya bayansa suna da “yancin bayyana ra’ayinsu”, kuma sun fahimci “rashin jin dadinsu” da matsayin kulob na bakwai.

“Mun san cewa kwallon kafa wasa ne na sha’awa da kuma jin dadi,” in ji kocin riko Rangnick. “Ina jin za mu iya fahimtar magoya bayanmu sun ji takaici tare da inda muka tsaya a tebur da kuma wasan da muka nuna a kan Everton.

“Amma na yi imanin cewa magoya bayanmu suna daya daga cikin mafi kyau a Ingila kuma idan har za su yi zanga-zangar ta hanyar lumana kuma tare da goyon bayan kungiyar a filin wasa ina ganin suna da ‘yancin bayyana ra’ayinsu. Zan iya. fahimci sun ji kunya.”

Kungiyar sun rufe ƙofofin shiga na yau da kullun a ƙoƙarin gujewa maimaita al’amuran shekara guda da ta gabata lokacin da magoya bayanta suka shiga manyan gine-gine, kuma daga ƙarshe sun yi ganawa da kociyan Ole Gunnar Solskjaer.

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Trending