Connect with us

Manyan Labarai

Na dan ji ba dadi da ka ja da ni a takarar fidda gwani – Tinubu

Published

on

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya ce, ya ji dan ba dadi da Sanata Ahmad Lawan shugaban majalisar dattawa ya ja da shi a zaben fidda gwani.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa, bayan ya samu nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a Abuja.

Tinu bu ya kuma ce”Abun kunya ne ga wadanda suke so su ga faduwar jam’iyyar APC a zaben 2023, domin kuwa APC na nan yadda take daram”.

“Shiru-shirun da na yi ba tsoro bane gudun magana ne, kuma a yanzu mun shirya gwabzawa da ko waye”.

“Shekaru 16 da PDP ta yi ta na barna a fadin kasar nan, yanzu ne lokaci ya yi da zamu samar da sabuwar Najeriya ga ‘ya’yan mu”

“Mu masu son ci gaba ne, mu masu son gina kasa ne, mu masu son kawar da duk wani abu da ya shafi kasar nan da al’ummar mu, mun shirya kawar da duk wanda ya shige mana gaba, gwamnonin da suka zabe ni ban san mai na yi na kirki da suka zabe ni ba, amma na san domin ci gaban kasa suka zaben ni. Za mu ci gaba da yakar duk wanda ya kawo tsaiko a Najeriya”.

“Yau rana ce da mata na 2, musamman ma Mama 60, bisa kwana da ta yi cir idanun ta biyu, ina godiya a gare ku”.

“Shugaban kasa ka yi hakuri da na sa ka kwana idanu biyu cir a wajen nan, kuma wannan lokaci ne ni ma da ya kamata ka rama min, tun da a baya ni ma na yi maka haka”.

 

Hangen Dala

Jami’ar Chikago ta baiwa Atiku bayanan Tinubu

Published

on

Jami’ar Jihar Chicago da ke Amurka ta saki takardun karatun Shugaba Bola Tinubu, bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar a a 2023 ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubukar ya buƙaci hakan.

 

A ƙarshen makon da ya gabata ne, wata kotun gunduma da ke arewacin Illinois a Amurka ta bayar da umarnin a sakarwa Atiku takardun karatun Tinubu.

 

A wani martani na buƙatar da Atiku ya miƙa a karo na uku, wanda ya nemi a saki kwafin sakamakon digiri 1977, Jami’ar ta ce takardun sun yi daidai da na Tinubu da ke ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Yunin 1977.

“Bayan bincike mai zurfi, Jami’ar CSU ta gano ta kuma gabatar da takardun da aka nema kuma ta gabatar da su don amsa wannan bukatar. Lambobin takardun su CSUO008 zuwa CSU0010.

 

“An shafe sunayen ɗaliban da ke kan takardun saboda a sakaya sunansu.

“CSU za ta kuma saki sakamakon daliban da suke kusa da shi, masu lamba CSU0011 da lamba 0017 na wasu ɗaliban bayan an doɗe sunayen (saboda a sakaye sunanyensu)”.

 

“Waɗannan takardun sun yi daidai da yadda na Tinubu, dalibin da aka yi wa sauyin makaranta yake,” kamar yadda jami’ar ta rubuta.

 

A baya Tinubu ya yi iƙirarin ɓatan ainihin takardunsa na jami’ar, abin da ya sa ya gabatarwa da hukumar zaɓe INEC wata takardar a matsayin madadin takardun na ainihi domin takarar shugabancin Najeriya a 2023.

 

Takardu da dama na waɗari a kafafen sada zumunta a matsayin shaidar kammala karatun na Tinubu a Jami’ar jihar Chicago.

 

Tambari da kuma bajon da jami’ar CSU ta saki na digirin a 1977 sun yi daidai da irin wanda Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC, sai dai an samu banbanci a kwanan wata.

 

Sai dai cikin bayanin da jami’ar ta yi, ta ɗauki alhakin kuskuren da aka samu a kwanan watan, tana cewa kuskure aka samu wajen rubutawa.

 

A ranar 19 ga watan Satumba ne, Jeffrey Gilbert na kotun majitare da ke Amurka ya amince da buƙatar da aka shigabar gaban kotun tare da ba da umarnin sakin takardun karatun Bola Tinubu cikin sa’a 24.

 

A wani ƙoƙari na ganin haka bai faru ba, Tinubu ya ɗaukaka ƙara kan wannan umarni.

Nancy Maldonado ta kotun tarayya ta sake tabbatar da wannan hukunci da Tinubu ya so ƙalubalanta, inda ita ma ta ce a saki takardun.

 

Domin bin umarnin kotun da cika buƙatar Atiku Abubakar CSU ta ce ba za ta iya nemo ainihin kwafin takardun da ta bai wa Tinubu ba 1979.

 

“A tsarin CSU ba ta ajiye kwafin takardun ɗaliban da suka yi digiri, kuma bayan dogon bincike ta gaza samo kwafin irin wanda ta bau wa Tinubu a 1979, don haka ba a samu takardun da aka buƙata ba,” in ji jami’ar.

 

Sai dai jami’ar ta saki takardun wasu ɗaliban da ta rufe sunayensu, waɗanda suka yi daidai da na Tinubu domin tabbatar da cewa ya kammala makarantar a baya.

 

Atiku Abubakar dai na son amfani da takardun ne a matsayin shaida a kotun ƙolin Najeriya kan ƙorafin da ya shigar game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a 2023.

BBC

Continue Reading

Manyan Labarai

Shekaru 63 na Nigeria:- Jawabin Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugabanni da saura al’umma da suyi koyi da tsaffin shugabannin da suka gabata wajen kawowa ƙasar nan ci gaba da zaman lafiya musamman a irin wannan lokaci.

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake jawabi kan cikar ƙasar nan shekara 63 da samun kyancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.

 

Gwamna Abba ya kuma ce la’akari da yadda ake tunawa da tsaffin shugabanni wajen ciyar da ƙasar nan gaba ya kamata su shugabannin yanzu suyi koyi da su.

 

 

Ka zalika ya ƙara da cewa ya kamata shugaban ni su tabbata sun yiwa al’umma abin da suke buƙata domin tabbatar adalci.

 

Gwamnatin tace zata ci gaba da gudanar da aikin ta kamar yadda ta tsara domin ciyar da Kano gaba.

Continue Reading

Hangen Dala

Hukuncin Kaduna :- PDP za ta daukaka kara

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tabbatar da zaben Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC, inda ta ce za ta garzaya kotun daukaka kara.

Alberah Catoh, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a a Kaduna.

Catoh ya ce, wani nazari da lauyan PDP ya yi ya nuna cewa hukuncin bai cika wasu ka’idoji na tabbatar adalci ba.

Martanin ya zo ne sa’o’i bayan kotun da ke zamanta a Kaduna ta amince da nasarar zaben Sani.

Ya kara da cewa hukuncin bai dace da wasu dokoki da ka’idojin zabe ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka jam’iyyar ta umurci lauyoyinta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja a cikin wa’adin da doka ta kayyade.”

Catoh ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP a fadin jihar da su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwarsu kan lamarin.

Continue Reading

Trending