Lafiya
Rahoto: Za mu ci gaba da taimaka wa al’ummar Tudun Kaba – Sakataren ilimi

Sakataren ilimi na karamar hukumar Kumbotso, Magaji Baure ya ce, son karatu ga al’ummar Tudun Kaba yasa hukumar ilimi ta taimaka musu da ajujuwan da za su rinka karatu tare da bandakuna.
Magaji Baure, ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abba Isah Muhammad, yana mai cewa, yanzu haka suna kokarin gina ofishin shugaban makarantar.
Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.
Labarai
Da Ɗuminsa: Ma’aikatan NAFDAC sun janye yajin aikin sati 6 da suka tsunduma

Ma’aikatan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), a ranar Litinin, sun dakatar da yajin aikin da suka kwashe makonni shida suna yi, a fadin kasar nan.
Ma’aikatan dai mambobin kungiyar ma’aikatan lafiya ne da ma’aikatan lafiya ta ƙasa (MHWUN).
Mataimakin shugaban kungiyar, Idzi Isua, ya tabbatar da faruwar lamarin, a yayin taron kungiyar a safiyar ranar Litinin. In ji Solacebase.
Isua ya ce, kungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan wata yarjejeniya da ta kulla da mahukunta.
Kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne a ranar 21 ga watan Yuni, 2022, domin nuna rashin amincewa da wasu abubuwa, rashin jin dadin jama’a da basussukan ci gaba da ba a biya ba.
Lafiya
Da Duminsa: Mun samu bullar cutar kyandar Biri a Katsina – Kwamishinan Lafiya

Gwamnatin jihar Katsina ta ce, ta samu bullar cutar kyandar Biri, yayin da ake jiran sakamakon wasu samfura guda 15 daga gwaje-gwajen da aka kai Abuja.
Kwamishinan lafiya na jihar, Injiniya Yakubu Nuhu Danja ne ya bayyana hakan, a ranar Talata a lokacin da yake kaddamar da rabon magungunan jinya kyauta tare da kaddamar da cibiyar kiran gaggawa a ofishin hukumar lafiya a matakin farko na jihar.
“Mun tabbatar da bullar cutar kyandar biri guda daya a jihar kuma an dauki dukkan matakan da suka dace, domin ganin an yi wa mara lafiyar magani. An sallami mutumin zuwa ga iyalansa.
“Muna da wasu mutane 15 da ake zargin sun kamu da cutar, kuma an kai samfurin su dakin gwaje-gwaje na kasa da ke Abuja, kuma ana sa ran sakamakonsu cikin mako guda,” in ji shi.
Labarai
NDLEA ta kama wata makauniya da ta tabar Wiwi buhu 24

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ta tabbatar da cafke wata ‘yar kasuwa mai suna Celina Ekeke, a unguwar Obunku, a karamar hukumar Oyigbo ta jihar Ribas.
Kakakin jihar Emmanuel Ogbumgbada, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, an kama matar da ake zargi makauniya ce, an kama ta da buhu 24 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 231.2.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022, da misalin karfe 2 na safe, jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen Etche na jihar Ribas sun gudanar da bincike a unguwar Obunku dake karamar hukumar Oyigbo inda suka kama wata Celina Ekeke, sanannen dillalin magunguna da buhu 24 na cannabis sativa mai nauyin 231.2kg.
“Ta kasance cikin jerin masu sa ido a hukumar tun da dadewa, inda take amfani da gurbatattun kafafunta wajen yin kwalliya da sayar da muggan kwayoyi. A yanzu haka tana gudanar da bincike a hedikwatar rundunar jihar Ribas.”
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai2 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya2 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano