Connect with us

Labarai

Karanta Labaran Dala na Yau Alhamis 18-04-2019

Published

on

Karanta Labaran Dala na Yau Alhamis 18-04-2019

                                    LABARAI A TAKAICE

Wani masanin zamantakewar dan adam dake Kwalejin Sa’adatu Rimi, Kwamared Auwal Rabi’u Babban Wando ya ce dabi’ar daukar hoto kafin aure wato pre-wedding pictures wanda matasa ke yi, bakuwar al’ada ce da suke kwaikwayo daga turawa wadda kuma zata iya bata rayuwar al’umma a wanan lokaci matukar ba’a kaurace yin hakan ba.

Kwamared Auwal Rabi’u Babban Wando ya bayyana hakan ne a ganawarsa da gidan Radiyon Dala, yana mai cewa shekarun girma da matasan suke kai, shi ne ke jan hankalin su wajen karkata kan al’amuran da suka shafi biyan bukatar sha’awa dake tsakanin mabambanta jinsi.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta bukaci al’umma da su rinka sanar dasu rahoton faruwar hadari domin kai daukin gaggawa cikin al’amarin kasancewar ya na daya daga cikin aikin hukumar.

Jami’in hulda da jama na hukumar, PFO Sa’idu Muhammad Ibrahim ne ya yi wannan kiran yayin ganawarsa da wakilin mu Hassan Mahmuda Ya’u, a kan wani kira da suka samu cikin dare sakamakon wani hadari da ya auku a kan titin Sharada, wanda ya jikkata wani mai babur yayin da suka yi taho mu gama da mai mota karshe a ka mika su zuwa asibiti cikin wani hali don ceto rayuwarsu.

Hukumar Hisba a nan jihar Kano, ta gargadi masu bada hayar gidaje dasu daina bada hayar gidaje ga mata masu zaman kansu ko kuma gauraya su da matan aure wuri guda.

Mataimakin hukumar kan nazarin manyan laifuka, Malam Idris Ibn Umar ne yayi wannan gargadi biyo bayan wani korafi da wata matar aure ta yi kan cewa wani mai bada hayar gidaje ya hadasu gida guda da mata masu zaman kansu inda ta bukaci ya sauya mata gida ko ya ba ta kudin ta abin ya gagara.

 

LABARAN DALA

18 04 2019.

LABARAI A TAKAICE.

Kakakin hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa a nan kano, Kabiru Ibrahim Daura, ya gargadi fasinjoji dasu kauracewa hawa motar da aka yiwa kazamin lodi da kuma masu gudun wuce sa’a, domin kiyaye rayuwarsu da kuma lafiyarsu.

Kabiru Ibrahim daura ya yi wanan jan hankalinne a ganawarsa da gidan radiyon Dala, kan wani hadari da kazamin lodi da gudun wuce sa’a suka haddasa, a ranar shida ga wannan watan kan titin zuwa Dan-batta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, bakwai kuma suka jikkata.

Rundunar ‘yan sandan jihar kano tace ta shirya tsaf don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’aumma ya yin gudanar da bukukuwan good Friday da Ista Monday.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun rundunar DSP Abdullai Haruna, ta rawaito cewa, rundunar ta kuma bukaci mutane su sanya ido kan bakin al’amrura tare kai rahoton duk wani abu da basu yarda dashi ba ga ofishin yansanda mafi kusa, tana mai jaddada haramcin fasa knock out yayin bukukuwan.

Mai Magana da yawun kotunan jihar kano baba jibo Ibrahim ya ce babban jojin jihar kano justice Nura Sagir Umar, ya bada hutu ga manayan alkalan kotunan jihar kano daga yau 18 ga watan Afirilu zuwa ranar 29 ga watan.

A zantawarsa da gidan radiyon Dala, Baba jibo Ibarahim ya ce hutun wanda bai shafi kotunan shari’ar musulinci ba, tanadi ne na kundin dokar tafikar da kotunan jihar kano ta shekarar 2014, karkashin oda ta 45.

Kotun Majistret dake zaman ta a Noman Sland a nan Kano, ta gurfanar da wasu mutane bakwai ciki harda wani mutum mai suna Muhammad Muntari, wanda ake zargin su da aikata laifuka wanda suka hada da mallakar manyan makamai ba bisa ka’ida ba da kuma yin fashi da makami tare da yunkurin yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Labarai

Ku guji tada hankalin al’umma yayin zaɓen ƙananan hukumomi a Kano – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta buƙaci al’umma musamman ma Matasa da su kasance masu bin doka da oda tare kuma da gujewa tayar da hankalin jama’a a yayin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da za ayi a yau Asabar.

Shugaban gudanarwar ƙungiyar na Ƙasa Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a safiyar Asabar.

Ya kuma ce bai kamata al’umma su kasance masu taka doka ba, domin bin doka shi ne wayewa.

“Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su bada gudunmawar su yayin zaɓen domin ganin an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin cikin kwanciyar hankali, “in ji Tasi’u”.

Da yake nasa jawabin daraktan ƙungiyar Kwamared Gambo Madaki, kira ya yi ga dukkanin ƴan ƙungiyar su na ƙananan hukumomin Kano 44, da ku guji sanya kayan ƙungiyar su yayin gudanar da zaɓen kasancewar ba sa cikin masu aikin zaɓen ko kuma sanya ido, domin gujewa fuskantar matsala.

Tuni dai hukumar zaɓe ta jihar Kano Kanseic, ta ce za’a fara kaɗa ƙuri’a ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar yau Asabar.

Continue Reading

Labarai

Sarkin Kano ya ɗaga likkafar Alhaji Abbas Ɗalhatu daga Ƴan Daka, zuwa Bauran Kano, da naɗa hakimai 10

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Alhaji Abbas Ɗalhatu shugaban rukunin gidajen Freedom Radio da Dala FM, a matsayin Bauran Kano, bayan da ya ɗaga likkafar sa daga Ƴan Ɗakan Kano.

Sarkin ya naɗa hakiman ne da safiyar yau Juma’a, inda ya kuma naɗa hakimai goma a matakai daban-daban, daga cikin su akwai Kacallan Kano, da Dan Adalan Kano, da mai unguwar Munduɓawa kuma hakimin Gezawa, da sauransu.

Da yake jawabi jim kaɗan da ɗin hakiman da kuma ɗaga likkar Alhaji Abbas Ɗalhatu zuwa Bauran Kano, mai martaba Sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce an naɗa hakiman ne bisa jajirecewar su da taimaka wa al’umma da kuma biyayya ga masarautar Kano.

Sarkin na Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya kuma hori dukkanin hakiman da su mayar da hankali akan samar da ci gaban al’ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Doragarai ya ruwaito cewa a yayin naɗin al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga ciki da wajen ƙasar nan.

Continue Reading

Trending