Connect with us

Labarai

LABARAN DALA22 04 2019

Published

on

LABARAN DALA

22 04 2019

LABARAI A TAKAICE

Dan dakan Karaye, kuma babban sakataren hukumar inganta tarihi da al’adun jihar Kano, Ibrahim Mua’azu, ya bukaci iyaye da su kasance masu kula da tarbiyyar ‘ya’yan su domin inganta rayuwar su.

Ibrahim Mu’azu, ya yi wannan kiran ne yayin bikin saukar karatun al’kurani mai girma na makarantar Abu Hurairai Islamiyya dake Lokon Makera a unguwar Kofar Na’isa.

Babban limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Jafar Mahmud Adam, dake unguwar Sabuwar Gandu, Mallam Abdullah Ishaq Abdullahi Garangamawa, ya yi kira ga al’umma dasu tashi tsaye wurin neman illimin addinin musulinci domin samun ingantaciyyar rayuwa da kuma tsira a gobe kiyama.

Malam Abdullah Ishaq Abdullah, ya yi wannan kiran ne yayin saukar Alkur’ani mai girma da makarantar Sheikh Jafar Mahmud Adam ta gudanar a unguwar Sabuwar Gandu a karshen makon da ya gabata.

A nan kuma limamin masallacin juma’a na Annur dake unguwar Zawachiki a karamar hukumar Kumbotso, Mallam Babangida Abba Giyade, bayyana cewa zance da ‘yan mata da samari ke yio kafin neman aure ba shine abin da musulunci ya bada umarni a yi ba, kawai dai jama’a na yi ne bisa masalahar kansu.

Mallam Babangida Abba Giyade, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin matattar Alheri na gidan rediyon Dala, ya ce ya kamata yayi a fara neman abokiyar zama kafin a yi aure.

Shugabar kungiyar tallafawa ‘yan gudun hijira ta Binta Muhammad Lawan ta yi kira ga sauran kungiyoyin al’umma da su rinka tallafawa ‘yan gudun hijira dake fadin jihar Kano baki daya.

Shugabar kungiyar Binta Muhammad ta bayyana hakan ne yayin rabon tallafin kayan more rayuwa da kungiyar ta rabawa ‘yan gudun hijira su kimanin 100 da suka ci gajiyar tallafin a sansanin su na dake unguwar Hotoro a nan Kano.

A wani labarin kuma wata kungiya mai rajin yaki da barace-barace, ta ja hankalin iyaye cewa dasu sauke nauyin da A… ya daura masu wurin lura da tarbiyyar ‘ya’yan su maimakon tura su yawon bara.

Babban jami’in gudanarwa na kungiyar reshen jihar Kano, Kwamrade Aliyu Samba ne yayi wannan kiran yayin taron gangamin wayar da kan iyaye kan barace-barace da kungiyar ta gudanar irin sa na farko a nan Kano.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kama wasu mutane hudu dauke da bindiga da wasu mutane biyu su na hadiyar hodar iblis a wani Otel a nan Kano a yunkurin su na safararta zuwa kasar Sudan da kuma kasar Saudiyya.

Da yake holin mutanen a karshen makon da ya gabata kwamandan hukumar ta NDLEA a nan Kano, Dr Ibrahim Abdul, ya bayyanawa manema labarai cewa kimanin watanni biyu suka shafe suna bibiyar masu yunkurin safarar hodar iblis din, wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa hukumar na kara neman hadin kai daga ‘yan kasa na gari.

 

Takaitattun labaran Dala Kenan….

 

Kada ku manta zaku iya samun sabbin labaran da muke sabintawa tsawon awanni ashirin da hudu a shafinmu na internet wato www.dalafmkano.com

 

Haka kuma zaku iya bayyana ra’ayoyinku ko tafka muhawara akan batutuwan da muke tattaunawa a dandalin Facebook da Twitter a Dala FM Kano.

Labarai

Rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi – Masanin tattalin arziki

Published

on

Wani masanin tatttalin arziki a jihar Kano Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, ya ce rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) kwandaloli, hakan kan haifar da koma baya musamman ma ga ƙasashen da basa amfani da su.

Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, wanda kuma shine shugaban sashin koyar da ilimin banking and finance na jami’ar tarayya ta Dutse, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Doka Gatan Al’umma na nan gidan rediyon Dala FM Kano, da ya gudana a yau Litinin.

“Dai na amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi, kuma idan mutum yaje sayen kayan masarufin zai fuskanci hakan, “in ji Dr. Ibrahim”.

Ya ƙara da cewa duk da cewar dai na amfani da ƙananun kudaɗen (Coins) da zarar an inganta harkar wutar lantarki, babu makawa za’a samu sauƙi saboda masu ƙananun masana’antu za su rage kashe kuɗi.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa Dakta Ibrahim Muhammad Ahmad, ya kuma bukaci hukumomi da su mayar da hankali akan noma da sanya kishin kasa a gaba, domin samar da ci gaba ga al’umma.

Continue Reading

Labarai

Zamu magance ƙalubalen da ake samu a fannin ilimi mai zurfi – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta sha alwashin mangance dukkanin wani ƙalubale a fannin ilimi mai zurfi a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Ibrahim Yusif kofar mata, ne ya
bayyana hakan a yayin taron yaye daliban kwalejin ilimi ta Aminu
Kano (AKCOE), da ya gudana a ranar Alhamis.

Y kuma ce yanzu haka tattaunawa tayi nisa a hukumance akan bukatar kwalejin dan ganin ta samu wadataccenf ilin da za ta gina jami’a.

Dakta Ibrahim kofar mata ya bayyana gamsuwa da tsarin da kwalejin take bi wajen gudanar da karatu, inda ya kuma ja hankalin dalibai 40 da suka karbi shaidar kammala karatun NCE,
da su zama ababen koyi.

Da yake nasa jawabin shugaban kwalejin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, ya ce da zarar sun shiga sabon tsari za su fara da daukar dalibai yan asalin jahar Kano mutum dubu daya kyauta, tare da biyawa ‘yan makarantar
kudi sama da Naira miliyan 300 yan asalin jahar kano dan
karfafawa matasa gwiwa.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka samu damar halartar taron daga guraren daban-daban na jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Labarai

Bama jin daɗin yadda wasu iyaye suke hana ƴaƴan su maza auren mu – Budurwa mai larurar Ƙafa

Published

on

Wata matashiyar budurwa mai buƙata ta musamman dake da lalurar Ƙafa Samira Ahmad Tijjani, ta nuna rashin jin daɗin ta, bisa yadda mafi yawan iyaye suke nunawa masu lalurar ƙyama, wajen hana ƴaƴan su auren masu lalurar ƙafar lamarin da yasa al’amarin ke matuƙar ɓata musu rai.

A zantawar wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, da budurwar ta ce, mafi yawancin su mata masu lalurar ƙafar sun ma fi mata masu lafiya iya Girki, da sauran ayyukan yau da kullum.

Ta ci gaba da cewa, “Amma abin takaici sai a rinƙa nuna mana ƙyama, ko kuma wariya musamman ma wajen neman aure, bayan kuma ba mu muka yiwa kan mu halitta ba, “in ji Samira”.

Ta kuma ce abinda wasu daga cikin iyaye suke yi musu kan nuna ƴaƴan su ba za su aure mai lalurar Kafa ba, basa jin daɗin hakan, shi yasa ma ta fito domin ta sanarwa al’umma domin gujewa hakan.

A cewar ta, “Ko nima nayi soyayya mara misaltuwa da samari masu lafiyar Ƙafa, amma mahaifiyar ɗaya daga cikin su ta ce ita ba wai bata sona ba, amma tana jin kunyar ta tuna ni a cikin mutane cewar a zummar matar ɗan ta”.

Daga bisani dai ta yi kira ga al’umma da su dai na nuna ƙyamar ko kuma nuna wariya a gare su, bisa yadda iyayen su suke matuƙar shiga cikin damuwa a duk lokacin da aka nuna musu wariyar.

Continue Reading

Trending