Connect with us

Lafiya

Hukumar NDLEA ta kaddamar da cibiyar kiran waya na kula da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi

Published

on

Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, (NDLEA), Birgediya. Janar Mohamed Buba Marwa Mai Ritaya, ya kaddamar da cibiyar kiran waya na zamani, domin kula da ‘yan Najeriya daga dukkan sassan kasar nan masu bukatu da suka shafi muggan kwayoyi.

Yayin jawabinsa a wajen taron, Marwa ya ce, masu shaye-shayen miyagun kwayoyi da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ba su da wani uzuri na rashin neman magani tare da kaddamar da cibiyar kiran waya mai aiki na sa’o’i 24 a kullum, domin kula da ‘yan Najeriya daga sassan kasar nan.

Cibiyar kira ta NDLEA mai layukan taimako kyauta na da ƙwararru da ƙwararru masu bayar da shawarwari, ilimin halin ɗan adam da wanda suke da tabin hankali da sauransu.

A cewar Marwa, “Samar da wannan layukan taimako kyauta, wani ci gaba ne a yunƙurin da muke yi na faɗaɗa hanyoyin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga masu shan muggan ƙwayoyi a ƙasar nan. Wannan ya zama wata larura da shiga tsakani a cikin yunƙurin da muka yi don shawo kan karuwar matsalar rashin amfani da muggan ƙwayoyi da kuma abubuwan da suka shafi kiwon lafiya. “

Ya ce duk da cewa, kasar nan na da cibiyoyin jinya, yayin da NDLEA na da wuraren jinya 26 a duk cikin umarninta, amma duk da haka ba su da isa sosai idan aka yi la’akari da kididdigar masu amfani da muggan kwayoyi da masu fama da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Lafiya

Likitocin da ke aiki da gwamnatin Kano sun jingine yajin aikin gargaɗin da suka fara

Published

on

Likitocin da suke aiki da gwamnatin jihar Kano (NAGGMDP), sun jingine yajin aikin gargaɗin da suka fara a ranar Talata 01 ga watan Oktoban 2024, biyo bayan wani zama da su ka yi da kwamitin da gwamnatin ta kafa.

Sakataren ƙungiyar Dakta Anas Idris Hassan Shanno ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kaɗan bayan kammala zaman gaggawa da su ka yi da ƴaƴan ƙungiyar.

Dakta Anas ya kuma ce sun ɗauki matakin jingine yajin aikin ne zuwa ƙarshen watan nan na 10, Kamar yadda gwamnatin ta dauki alkawarin cewa za ta biya masu buƙatun su a lokacin.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa ƙungiyar ta kuma buƙaci dukkanin likitocin da ke ƙarƙashin ta da su koma bakin aikin su.

Continue Reading

Lafiya

An ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta a Kano

Published

on

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da unguwar zoma ta ƙasa reshen asibitin Ƙashi na Dala a jihar Kano, ta ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta ga al’umma.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya na asibitin Ƙashi na Dala, Kwamared Abubakar Muhammad Isah, ne ya bayyana hakan a wani ɓangaren na tunawa da bikin ranar ma’aikatan jinya ta Duniya, wanda a nan Kano za’a shafe mako guda ana gudanar wa a jihar Kano.

Kwamared Abubakar Muhammad, ya kuma ce sun zaɓi gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta, domin saukakawa al’umma.

A cewar sa, “Mutane ku rinƙa zuwa Asibiti ana gwada lafiyar ku ba sai baku da lafiya za ku je gwaji ba domin mai lafiya shine yake neman magani dan ya yi rigakafi, amma da zarar cuta ta ci karfin mutum to lamarin ya yi munin gaske, “in ji shi”.

Wakilinmu Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar kungiyar za ta kwashe mako guda tana gudanar da taruka dan wayar da kan al’umma a kan batun lafiya.

Continue Reading

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Trending