Connect with us

Lafiya

Da Duminsa: Mun samu bullar cutar kyandar Biri a Katsina – Kwamishinan Lafiya

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta ce, ta samu bullar cutar kyandar Biri, yayin da ake jiran sakamakon wasu samfura guda 15 daga gwaje-gwajen da aka kai Abuja.

Kwamishinan lafiya na jihar, Injiniya Yakubu Nuhu Danja ne ya bayyana hakan, a ranar Talata a lokacin da yake kaddamar da rabon magungunan jinya kyauta tare da kaddamar da cibiyar kiran gaggawa a ofishin hukumar lafiya a matakin farko na jihar.

“Mun tabbatar da bullar cutar kyandar biri guda daya a jihar kuma an dauki dukkan matakan da suka dace, domin ganin an yi wa mara lafiyar magani. An sallami mutumin zuwa ga iyalansa.

“Muna da wasu mutane 15 da ake zargin sun kamu da cutar, kuma an kai samfurin su dakin gwaje-gwaje na kasa da ke Abuja, kuma ana sa ran sakamakonsu cikin mako guda,” in ji shi.

Lafiya

PCN ta lalata magunguna na Naira miliyan 100 bayan wa’adin su ya kare

Published

on

Hukumar Kula da Magunguna ta Kasa (PCN), ta lalata magungunan da suka wuce na sama da Naira miliyan 100 a jihar Adamawa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin cewa, an tattara magungunan da wa’adin su ya kare daga shagunan sayar da magunguna daban-daban a fadin jihar.

Wakilin kakakin majalisar dokokin jihar, Iya Aminu Abbas ne ya jagoranci lalata magungunan da aka yi a wajen garin Yola mai suna Conerwire, daura da hanyar Yola-Numan.

Mataimakin shugaban majalisar, Pwamakino Mankendo, wanda ya tsaya a madadin Abbas, ya yabawa kungiyar masu harhada magunguna ta kasa reshen jihar Adamawa kan yadda suka hana sayar da magungunan da wa’adin su ya kare zuwa cikin kasuwa.

Shima da yake jawabi yayin atisayen lalata magungunan, kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Adamawa, Femi Agbolu, ya ce, abin farin ciki ne a gano magungunan tare da lalata su.

Tun da farko, Shugaban Hukumar PCN na jihar, Ibrahim Talba ya ce, an kama magungunan ne daga sassan jihar a wani bangare na kokarin kawar da magungunan da wa’adin su ya kare da na jabu.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Amfani da Turoso a gona ya na da illa a jikin Dan Adam – Malamin Jami’a

Published

on

Wani malami a tsangayar koyar da aikin gona da ke jami’ar Bayero a jihar Kano, Malam Abubakar Adamu, ya ce, amfani da Turoso a gona yana da illa a jikin Dan Adam.

Malam Abubakar Adamu, ya bayyana hakan ne, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Yusuf Nadabo Isma’il.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Lafiya

A na zargin matashi da kashe kishiyar mahaifiyarsa tare da karya mahaifinsa

Published

on

Wani matashi mai suna Najeeb Shehu Umar, mai shekaru 24, dalibi mai matakin aji na 300 a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma a na zarginsa da kashe kishiyar mahaifiyarsa har lahira a gidansu da ke Ambassadors Quarters, Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce Najeeb ya kuma karya kafar mahaifinsa da hannu a lokacin da ya yi kokarin shiga lamarin, wanda ya jefa mazauna unguwar cikin rudani.

Mahaifinsa, Shehu Umar Balele, wanda shi ne mai kula da ma’aikatar ilimi ta Katsina, an ce yana karbar kulawar likitoci a sashin kula da kashi na asibitin koyarwa na Katsina, kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana wa Daily Post.

An rawaito cewa Najeeb a lokuta da dama ya nuna rashin jin dadinsa ga Hajiya Hasiya Galadima mai shekaru 65 da haihuwa tsohuwat ma’aikaciyar gwamnatin jihar Katsina.

An ce Najeeb, wanda ya taba yin ta’ammali da miyagun kwayoyi, a lokuta da dama ya sha yin barazanar kashe kishiyar mahaifiyarsa, bisa zargin cewa ita ce ke da alhakin raba shi mahaifinsa da mahaifiyarsa.

Babban yaron gidan, Mustapha Shehu Umar wanda shi ma yana zaune a gidan tare da matarsa ​​da ‘ya’yansa, yayin da yake tabbatar da rahoton ga DAILY POST, ya kuma bayyana cewa, dan uwansa, Najeeb ya yi barazanar kashe mahaifiyarsu a lokuta da dama, amma mahaifinsu ya hana su daukar mataki a kansa domin yana son yayi karatu.

Sai dai kuma a irin wannan lokacin, sai da suka kai rahoton barazanar ga ‘yan sanda, amma ba a dauki wani mataki na zahiri a kansa ba.

Da yake ba da labarin abin da ya faru, Mustapha ya ce, dan uwansa wanda ya ke da shaye-shaye iri-iri, ya kai wa mahaifiyarsu hari a dakinta a lokacin da danta tilo ya zo gidan dangin.

“Najeeb ne ya shiga falon uwar gidan mu rike da makami ya kulle kofar shiga. Ya tuna mata alkawarin da ya yi zai kashe ta. Sannan ya buge ta a kai da gwaggo har sau biyu sannan ta fadi.

“Yar uwata da ke tare da mahaifiyarmu a zaune, ta ruga ta rike shi. Suna ta faman tureshi. Sannan ta ruga ta bude kofar shiga ta fita da gudu. Yana cikin kiran agaji ya tashi ya bi bayanta, amma da sauri mahaifinmu ya sa baki da gudu daga dakinsa ya kasa zuwa wajenta. Duk da haka, ya sa wa mahaifinmu duka, ya karye masa ƙafa don ƙoƙarin hana shi.

 

Continue Reading

Trending