Connect with us

Manyan Labarai

Takarar Muslumi da Musulmi: Lauya ya kai karar APC da Tinubu kotu

Published

on

Wani lauya mazaunin Abuja, Osigwe Momoh, ya maka jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu kara, a kan tsayar da musulmi dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Tinubu ya zabi Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023. Wannan ci gaban ya haifar da fushi daga manyan masu ruwa da tsaki, musamman kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1188/2022 da aka shigar a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja, Momoh na neman a ba da umarnin har abada hukumar zabe ta kasa (INEC) daga buga sunan Tinubu a zabe mai zuwa.

Ya ce, jam’iyyar APC ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, ta hanyar zabo dan takararta na shugaban kasa da abokin takararsa daga addini daya.

A farkon sammacin, mai shigar da karar ya bayyana cewa, bisa ga babi na biyu na kundin tsarin mulkin tarayya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), dole ne jam’iyyun siyasa su samu ‘yan takararsu na shugaban kasa da na mataimakin shugaban kasa daga bangarori daban-daban na kabilu da na addini.

Saboda haka, ya roki kotun da ta bayyana cewa, “Bisa ga sashi na 14 (1) & (3), 15 da 224 (a) na kundin tsarin mulkin tarayya na 1999, (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima), wadanda ake kara suna da hakkin su. Ka’idojin Babi na II na Kundin Tsarin Mulki na 1999 kamar yadda aka gyara da samun ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakan shugaban kasa na addini daya ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa kuma ba komai bane”.

Momoh yana kuma neman odar “Soke takarar APC, Tinubu (daya cikin 2), wanda ya sabawa kundin tsarin mulki kuma ya saba wa ruhin sashe na 14 (1) & (3), 15 da 224 (a) na 1999 da aka gyara. Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya”.

Har yanzu ba a sanya ranar da za a saurari karar ba.

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya yi alƙawarin gyara titin garin Kundila da ke ƙaramar hukumar Shanono

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawari gyara titin da ya taso daga babban titin karamar hukumar Shanono zuwa garin Kundila da ke karamar hukumar.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan yayin ta’aziyyar da ya kai na rasuwar ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono Honorable Halilu Ibrahim Kundila.

Marigayin dai ya rasu ne a makon da ya gabata.

Gwamna Abba Kabir Yusif ya kuma bayyana kaɗuwar sa a lokacin da yaji rasuwar Marigayin, inda ya ce mutum ne mai gaskiya da rukon amana.

Wakilinmu na fadar gwamnatin jihar Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Abba Kabir ya kuma ce gwamnatin Jihar Kano za ta dauki nauyin karatun iyalan mamacin daga inda suka tsaya har su kammala karatun nasu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Fitacciyar Jarumar Kannywood Saratu Giɗaɗo (Daso) ta rasu

Published

on

Fitacciyar Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Saratu Gidaɗo wadda akafi sani da Daso, ta rasu a yau Talata.

Mijin ƙanwar marigayiya Daso, kuma mai baiwa gwamnan Kano shawara a kan harkokin tafiye-tafiye da shaƙatawa Mustapha Ibrahim Chidari, ne ya tabbatar wa wakilinmu Bashir Sharfaɗi rasuwar ta a ranar Talata.

Ya ce da Asubar yau tayi Sahur, ta koma Bacci, sai dai kuma zuwa wajen ƙarfe 10 na safe aka ga bata fito daga ɗakin ta ba, ko da aka shiga ɗakin ne aka tarar ta rasu.

Mustapha, ya ce za’a yi jana’izar ta da yammacin Talatar nan, da misalin ƙarfe 04:30 a gidanta dake Chiranchi cikin garin Kano.

Marigayiya Daso, guda ce daga cikin fitattun jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wadda ta shafe shekaru a masana’antar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Doka za ta yi aiki akan duk masu tayar da hankalin al’umma yayin bikin Sallah – Ƴan Sandan Kano.

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ba za ta saurarawa ɓata garin da suka ce ba za’a zauna lafiya ba, a yayin bikin ƙaramar Sallah.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakiliyar mu A’isha Shehu Kabara, ya ce duk wasu gungun mutane da suka ce zasu ɗaukko muggan makamai da zummar tayar da hankalin al’umma ko kuma illata mutane lashakka doka za tayi aiki a kan su.

“Duk wanda ya ce ba za’a zauna lafiya ba a yayin bikin ƙaramar Sallar mu kan mu ba zamu bar shi ya nutsu ba, za muyi duk abinda ya kamata na ganin cewa an kare irin waɗannan abubuwa, “in ji SP Kiyawa”.

Ya ƙara da cewa yanzu haka Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya riga ya bada umarnin baza jami’an tsaron ƴan sandan su, kuma ciki har da na farin kaya da kuma wadata su da kayan aiki, domin yin dukkan abinda ya kamata wajen ganin an tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Rundunar ƴan sandan Kano, ta kuma shawarci masu ababen hawa da su kula yayin tuƙi a kan hanya da cikin unguwanni a yayin bikin ƙaramar Sallah, tare da kaucewa gudun ganganci, domin kaucewa afkuwar haɗura.

“Iyaye ku kula da ƴaƴan ku a yayin bikin sallar domin gujewa ɓatan su ko kuma faɗawa komar ɓata gari, a cewar sa”.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake sa ran gudanar da bikin ƙaramar Sallah, a ranar Laraba 10 ga watan Afrilu na shekarar 2024.

Continue Reading

Trending