Connect with us

Labarai

Hukumar kare hakkin mai saye ta kama gurbataccen taki da garin tuwo a Kano

Published

on

Hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta jihar Kano, karkashin jagorancin Dr. Baffa Babba Dan Agundi, ta samu nasarar gano wani rumbun ajiyar kayayyaki a garin Gunduwawa Makare da takin zamani wanda ake zargin gurbatacce ne.

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano a hukumar, Salisu Muhammad wanda ya wakilci Babbaf Baffa Dan Agundi, ya bayyana hakan cewa, a na zargin masu wajen suna yin gurbataccen takin ne a wajen, ta hanyar gauraya takin mai kyau da kasa, sannan suna fitar da shi kasuwanni, domin sayar wa manoma, a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Aminu Yakasai ya sanyawa hannu.

Salisu Muhammad ya kuma ce, hukumar ta sake gano wani wajen a karamar hukumar Garko, wanda shi ma a ke yin irin wannan almundahanar takin zamanin.

Haka zalika, hukumar ta samu nasarar kama wata babbar mota cike da buhunhunan garin Samanbita, wanda shi ma a ke zargin lalatacce ne an shigo da shi za a kai kasuwannin Kano.

Ya tabbatar da cewa, dukkan wadannan nasarori an same su ne a cikin makon da ya gabata, sakamakon bayanan sirri da hukumar ta samu daga wasu masu kishin jihar Kano.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending