Connect with us

Labarai

Atiku ka yi amfani da ƙwarewar ka na ceto Najeriya – Sarkin Adamawa

Published

on

Sarkin Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, ya ce, ya na da yaƙinin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya na da gogewar da zai iya riƙe Shugabancin kasar nan.

Sanarwar mai ƙunshe da sa hannun, Abdulrasheed Shehu, mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai, wanda ya rabawa manema labarai, Sarkin ya ce.

Ina addu’ar samun nasarar Atiku a zabe mai zuwa da kuma nan gaba, kuma ya yi amfani da kwarewar sa wajen mulki, domin sakewa kasar nan saiti al’amarin da zai kyautata tsaro da da zaman lafiyar kowa, masarautar Adamawa na alfahari da kai saboda nasarorin da ka cimma, wajen hada kan kasa da gina al’umma.

A jawabin sa, Atiku Abubakar wanda ke rike da sarautar Wazirin Adamawa, mukami na biyu mafi girma a masarautar, ya bayyana matukar jin dadi, saboda kasancewar sa a gida, domin sake dunkulewa da mutanen sa.

A ziyarar nai cike da tarihi da Atiku ya kai masarautar, ta sami halartar manyan mutane daga sassan kasar nan, ciki harda tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Namadi Sambo da shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu da mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Ifeanyi Okowa da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu da tsohon gwamnan Adamawa Boni Haruna sai kuma sarakunan Mubi da Ganye da sauran masarautun jihar ta Adamawa da sauran abokan Atiku Abubakar.

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Trending