Labarai
LABARAI A TAKAICE
2:22pm Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta tabbatar da cewa a shirye ta ke tsaf domin dakile masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a fadin jihar Kano.
Jim kadan bayan kammala shirin dansanda da jama’a, Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kuma kara da cewar ”rundunar ta dauki matakin gudanar da binciken motoci musamman masu sanyawa gilashin motar su duhu ba bisa doka ba”.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Sharada United dake karamar hukumar birni a nan Kano, Rabi’u Muhammad Datti wanda aka fi sa ni da Rabio’u CanhRabio’u Canhuu, ya ajiye aikin sa na jagorancin kungiyar.
Rabi’u Canhu, a wata sanarwa da ya yi a shafin sada zumunta na watsapp na kungiyar da yayi a cikin makon nan, ya ce ”ya ajiye aikin nasa ne sakamakon wasu dalilai wanda har yau bai kai ga bayyana su ba”.
2:15pm Gwamnatin jihar Kano ta amince da nada sabbin kwamatin riko na kasuwar ‘Yankaba dake nan jiha.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar kasuwanci, Salisu Babangida ya sanyawa hannu, ta ce mutum tara ne zasu jagoranci kwamatin wanda suka hada da mashawarci na musamman ga gwamnan Kano a kan kungiyoyi, Muhammad Najeeb Abdullahi a matsayin shugaba sai Alh Uba Sarina a matsayin sakatare.
Gwamnatin jihar Kano, ta mayar da asibitin Abdullahi Wase wanda aka fi sani da asibitin Narsawa zuwa asibitin koyarwa na kwararru na Yusuf Maitama Sule.
Yayin da yake ganawa da manema labarai, Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Farfesa Ahmad Mustapha, yace ”gwamnatin jihar Kano ta baiwa jami’ar Asibitin ne sakamakon kwas din aikin likita da jami’ar za ta fara a nan gaba”.
Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON)ta gudanar da taron wayar da kan jami’an hukumar dake jibintar aikin hajji a fadin kasar nan.
Jim kadan bayan kammala taron da ya gudana a jihar Kano cikin makon nan, shugaban sashin koyarwa da ilmantarwa na hukumar, Ahmad Imam Sa’ad, ya ce ”taron sun shirya shi ne don tunatar da jami’ai tare da sun wayar da kan alhazan bana”.
Wani masanin zamantakewar dan Adam dake kwalejin Sa’adatu Rimi a nan Kano, Kwamrade Auwal Rabi’u Babban Wando, ya ce ”ya zama wajibi iyaye sai sun tashi tsaye a kan kula da tarbiyar ‘ya’yan su musamman ta bangaren amfani da wayar salula”.
Kwamrade Rabi’u Babban wando ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin wannan rayuwa na gidan Rediyon Dala, ya kuma ce ”har idan iyaye zasu ke sanya idanu ga ‘ya’yan su yadda suke amfani da wayar salula ta hanyar shiga yanar gizo to babu makawa zai magance lalacewar tarbiyar su da ma al’adun malam bahaushe”.
Kada ku manta zaku iya samun sabbin labaran da muke sabintawa tsawon awanni ashirin da hudu a shafinmu na internet wato www.dalafmkano.com
Haka kuma zaku iya bayyana ra’ayoyinku ko tafka muhawara akan batutuwan da muke tattaunawa a dandalin Facebook da Twitter a Dala FM Kano.

Labarai
Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.
Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.
Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.
A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Labarai
Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.
Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.
“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.
Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.
Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Labarai
Za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 – Masani

Wani masanin ilmin Taurari da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Mallam Nasir Falaki Al-Kanawi, ya ce za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 saboda watan Shawwal ba zai ganu ba a ranar Asabar, don da ƙarfe 11:58 na safe za a haifi jinjirin watan kuma zai faɗi 06:48 na Yamma.
Mallam Nasiru Alfaki Al-Kanawi ya bayyana hakan ne a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Juma’a 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.
Alfalaki ya kuma ce watan zai faɗi ne da ƙarfe 6:48 na yamma mintuna kasa da 10 kenan bayan faduwar Rana, kasancewar ranar ƙarfe 6:37 na yamma za ta fadi.
Ya ci gaba da cewa to wannan dalilin ne zai sa watan ba zai ganu ba, ko da kuwa da Na’ura ne kasancewar bai samu wadataccen hasken da zai ɗosana daga ranar ba, wanda aƙalla yana buƙatar awanni 13 zuwa 16 daga haifeshi kafin ace an iya ganinsa, Allah shi ne mafi sani Mai iko akan komai.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su