Connect with us

Labarai

Badakalar Biliyan 20: Marwa ka gaggauta gurfanar da jami’an NDLEA – HURIWA

Published

on

Kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil’adama ta kasa (HURIWA), ta bukaci shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, da ya fallasa tare da gurfanar da jami’an NDLEA dake da hannu a wata badakalar karkatar da miyagun kwayoyi na Naira biliyan 20 na kasafin kudin hukumar.

Ko’odinetan HURIWA na kasa, Kwamared Emmanuel Onwubiko, a cikin wata sanarwa, ya ce yawancin jami’an hukumat akwai nagari da su ke da ƙwazo, amma hukumar ta sani cewa, ta gaggauta gurfanar da gurbatattun cikin su.

Bayanin na kungiyar ya biyo bayan wallaf wani bidiyo da aka yi a ranar Juma’a, 25 ga watan Agusta, 2022, mai taken, ‘Yadda Jami’an NDLEA suka karkatar da kudaden kasafi na Naira biliyan 20 da sauran kudade.

Rahoton ya ruwaito wani babban jami’in hukumar ta NDLEA da ba a bayyana sunansa ba, ya na zargin cewa, jami’an hukumar sun karkatar da sama da Naira biliyan 20 daga cikin kasafin  da wasu kudade daga hukumomin bayar da agaji da aka tanada, domin ci gaba da gudanar da ayyukanta a jihohi daban-daban na tarayya.

Jami’in da ba a bayyana sunansa ba, kamar yadda rahoton ya bayyana, ya kuma ce kimanin watanni 18 da nadin Marwa a matsayin shugaban hukumar ta NDLEA, an rubuta alamomin da suka hada da sama da Naira biliyan 38 da hukumar ta samu a shekarar 2022, da kashe kudi, inganta sama da kashi 70 na ma’aikata, daukar sabbin ma’aiakata 5,000, da dai sauransu.

Da yake tsokaci, Onwubiko na HURIWA ya ce, “Dole ne a binciki yadda hukumar ta NDLEA ta bayyana ra’ayinta mai cike da rudani, kuma dole ne a kama jami’an da ke da hannu, domin gurfanar da su a gaban kuliya a yanzu.

HURIWA ta bukaci shugaban hukumar ta NDLEA, Buba Marwa da ya tabbatar da bayyana cikakken bayani kan zargin almundahanar Naira biliyab 20 da sauran almundahana.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending