Connect with us

Labarai

An fara shari’ar mutumin da ake zargi da cin naman mutane a Makurdi

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 45 dan asalin jihar Benue a gaban wata kotun Majistare da ke Makurdi, bisa zarginsa da laifin cin naman mutane.

Jeremiah Ode, dan Igwe Ochekpo a karamar hukumar Oju, wanda aka kama yana cin kan wata mata da ake zargin ya kashe ta a gonarta, ana tuhumarsa a gaban wata kotun Majistare da ke Makurdi, bisa laifin kisan gillar da aka yi wa Priscilla Adoga, ‘yar shekara 65.

Sufeto Omaye Ujata, jami’in ‘yan sanda mai shigar da kara, ya shaida wa kotun cewa lamarin wanda ya faru a ranar Juma’a, 19 ga watan Agusta, Silas Igiri na karamar hukumar Oju ya kai rahoton ga ‘yan sanda.

A cewar rahoton Igiri, wanda ake zargin ya je gonar da matar kawunsa, Priscilla, ke aiki, ya kashe ta ta hanyar amfani da adda.

Bayan ya yanke kan Priscilla, sai ya shirya barkono da ita nan da nan kuma yana ci lokacin da aka kama shi.

Wasu majiyoyi a yankin sun shaida wa manema labarai cewa, a lokacin da Priscilla ba ta dawo daga gona a daidai lokacin da aka saba ba, sai ‘yan uwanta suka je nemanta, sai kawai suka tarar da Irmiya, wanda aka san shi da ciwon hauka, yana cin kan matar. .

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya yi haka, Irmiya ya ce, ya fara da kai ne kawai daga nan zai wuce zuwa jikinta.

Lokacin da ‘yan sandan suka bukaci ya bada labarin faruwar lamarin, Jeremiah ya bada labarin yadda shi da Priscilla suka yi artabu da adduna har sai da ya ci karfin ta.

Wani shafin intarnet na Benuwe, Stateflash ya bayyana cewa “’yan sanda sun dauki labarin ya zama kamar na mahaukaci, don haka, sun yanke shawarar gurfanar da shi a gaban kuliya.

“Ko da yake mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa, wanda ake tuhuma ya amsa laifin aikata laifin, ba a kai kara ba, saboda rashin hukumci”.

Domin haka babban alkalin kotun, Misis Regina Algh, ta bayar da umarnin a garkame wadanda ake zargin a gidan yari na tarayya dake Makurdi.

Ko da yake kotun ta ki amincewa da hurumin sauraron karar, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, lokacin da aka ambaci karar.

An dage sauraren karar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, domin samun shawarwarin shari’a daga ma’aikatar shari’a ta jihar.

 

Labarai

Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.

Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.

Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.

Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala

Published

on

Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.

“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.

Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.

Continue Reading

Labarai

Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge

Published

on

Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.

Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.

Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.

A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.

Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.

Continue Reading

Trending