Connect with us

Labarai

Labarai a takaice na yau Talata 30 04 2019

Published

on

5:54 Daliban Jamiar Yusuf Maitama Sule dake nan Kano tare da hadin gwiwar sauran daliban Jami’oi daban daban dake sassa daban-daban na fadin kasar nan tare da hadin kan wasu ‘yan kungiyoyi suka gudanar da wata Zanga-zangar lumana a cikin akwaryar birnin Kano.

Zanga Zangar dai ta samo asali ne bisa zargin wata daliba mai suna Zainab Habibu Aliyu ‘yar asalin jihar Kano da Kasar Saudiyya ta kama ta da kwaya a cikin Jakarta, zanga-zangar sun yi ta ne har zuwa gidan Gwamnatin Jihar Kano domin kai koken su Inda suka sami tarba daga Sakataren Gwanatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji a madadin Gwamnan Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje daga nan su ka wuce zuwa ofishin jakadancin kasar Saudiyya dake jihar Kano.

A wani cigaban kuma tuni kasar Saudiyya ta saki dalibar Zainab Habiba Aliyu aka kuma mika ta zuwa ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar Saudiyya bayan da gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamarin inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugaban alkalin alkalai Tanko Muhammad da ya hanzarta shiga cikin lamarin.

Kungiyar likitocin dabbobi ta kasa reshen jihar Kano, ta ce ana iya daukar cutar dabbobin gida har idan suna dauke da wata cuta musamman ma mai saurin yaduwa.

Mataimakin shugaban kungiyar, Dr Aminu Bello Hanga ne ya tabbatar da hakan yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala, ya na mai cewa ”kamata ya yi mutane da su rinka taka tsantsan da dukannin nau’ikan dabbobin da su ke mu’amala dasu musamman ma a lokacin da suka ga wani sauyin yanayi ga dabbobin su”.

Tsohon shugaban makarantar Kwalejin Rumfa dake nan Kano, Malam Tijjani Muhammad Adam, ya yi kira ga tsofaffin dalibai, da su ci gaba da hada kai tare da samarwa makarantun da suka kammala hanyoyin ci gaba.

Malam Tijjani Muhammad Adam, ya yi wannan kiran ne yayin taron tsofaffin daliban makarantar Kwalejin Rumfa aji na shekarar 1998, yayin taron an karrama tsofaffin ‘ya’yan kungiyar wanda suka hada da Dr. Ashir T. Inuwa na sashin koyar da aikin jarida a jami’ar Bayero da ya kammala digirinsa na uku, da kuma Dr. Musbahu Haruna Ahmad, wanda shima ya zama kwararre a bangaren kwakwalwa da laka a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Mataimakin babban Sufetan ‘yansanda na kasa mai kula da shiyya ta daya, AIG Danbature, ya bude dakin taro na rundunar ‘yansanda ta jihar Kano wanda kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Muhammad Wakili ya sabunta dakin taro a shalkwatar rundunar dake unguwar Bompai.

Taron wanda ya sami halartar manyan jami’an ‘yansanda da kanana da sauran al’ummar gari, inda aka sanyawa dakin taron suna IGP Muhammad Abubakar Adamu, wannan dai na daya daga cikin ayukan da CP Muhammad Wakili yake gudanarwa a jihar Kano bawai iya akan kwaya ya tsaya ba.

Mai Magana da yawun ma’aikatan gidajen yari na jihar Kano, DSP Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, yace sashi na dari uku da casa’in da tara na kundin tafikar da tsarin aikin ma’aikatan gidan yari ya baiwa kowane dan kasa damar kai ziyara tare da bada gudunmawa ga dauraru.

DSP Musbahu, ya ce ”a don haka kowa na da damar kai gudunmawarsa ga daurarru tare da kai masu ziyara a fadin kasar nan”.

Limamin massalacin juma’a na Khulafa’urrashidin dake unguwa uku ‘yan awaki, Malam Muhammad Sani Umar Arqam, ya gargadi ‘yan kasuwa da su rinka sassauta farashi don saukakawa al’umma musamman ma a watan Ramadan mai karatowa nan da wasu ‘yan kwanaki.

Ta cikin shirin shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala, a nasa bangaren Malam Yusuf Abdulrahman Yusuf Uba Mandawari wanda ya kasance a cikin shirin, ya bayyana cewa ”matsalar tsaro da ake fama da ita, na da nasaba da talaucin da mutane suka tsinci kan su a ciki”.

Wani kwarraren likita dake aiki a asibitin koyarwa na Aminu Kano, Dr Ibrahim Danjummai, ya shawarci masu dauke da cutar ciwon sukari dasu kaucewa cin abubuwan da za su rinka tayar da masu da cutar su musamman ma cin kitse.

A zantawarsa da gidan rediyon Dala, Dr Danjummai, ya kuma ce ”wadanda basu da wannan cuta sai sun kasance masu motsa jiki akai-akai don gudun kamuwa da cutar ciwon suga”.

 

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Labarai

Abin takaici ne yadda ake fuskantar ƙarancin ruwan Sha a sassan jahar mu – Gwamnan Kano.

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nuna rashin jin daɗin sa bisa yadda ake samun ƙarancin Ruwan Sha, a wasu daga cikin sassa jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, a lokacin a ya kai ziyarar gani da ido, matatar Ruwa da ke Tamburawa a yammacin yau Juma’a, a ƙokarin sa na na gyara ɓangaren ruwan a cikin garin Kano.

Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma sha alwashin tabbatar wa al’umma cewar, gwamnatin sa za ta yi aiki ba dare ba rana domin tabbatar da isasshen ruwan Sha ga al’ummar jihar Kano.

Gwamnan ya ƙara da ce a lokacin da suka zo ba sufi mako biyu ba suka samar da ingantaccen Ruwan sha, wanda ya rinƙa shiga cikin lunguna da Sako na sassan jihar.

Continue Reading

Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da sayar da Burtalai a wasu garuruwan ta

Published

on

Biyo bayan kokawar da wasu Fulani Makiyaya suka yi kan yadda wasu suka gididdiba burtalai yayin da aka siyarwa Manoma, a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, yanzu haka ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da taɓawa, ko kuma sayar da dukkanin Burtalan kiwon shanun ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban riƙon ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu a kan taɓa dukkan guraren, a dan haka sun dakatar da dukkanin yunƙurin taɓa Burtalan har sai shugabanni na kwamitin ƙasa sun kammala bincike wanda yanzu haka ake ci gaba da yi.

Da yake nuna jin daɗin sa kan matakin dakatarwar, amadadin Fulanin garuruwan, shugaban ƙingiyar Funali Makiyaya ta Gan Allah, Ahmad Shehu Gajida, yabawa gwamnatin jihar Kano, da kuma ƙaramar hukumar ta Tofa ya yi, bisa karɓar koken su da suka akai.

A baya-bayan nan ne dai a zantawar Dala FM Kano, da wasu Funalani Makiyaya mazauna garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, suka koka kan yadda aka gididdiba burtalan a yankunan nasu aka siyarwa manema, lamarin da suka ce ka iya sawa su rasa guraren da za suyi kiwon shanun su wanda hakan babbar barazana ce a gare su.

Continue Reading

Trending