Labarai
Hisba: Kallo ya koma sama a kan Barasa

Dakarun hukumar Hisba, sun samu nasarar kwato motar Barasar da suka kama a kan titin zuwa Zaria a jihar Kano, bayan tun a farko a ka yi zargin wasu jami’an tsaro sun hana su kama motar harma a na zargin an yi dauki ba dadi.
Rahotanni daga shelkwatar hukumar Hisba, na nu da yadda jami’an tsaron su ka yi wa harabar tsinke, sakamakon haushin kwace motar da su ka yi har zuwa ofishin Hisba.
Nan gaba za mu ji martanin hukumar Hisba, dangane da halin da a ke ciki na kama motar Barasar da su ka yi.

Labarai
Kanikawa sun fara Dariya a Kano kan saukar farashin man Fetur a Najeriya

Wani mai gyaran motoci a jihar Kano, da ke arewacin Najeriya, mai suna Abubakar Abdullahi, ya ce biyo bayan raguwar farashin litar fan fetur da ake samu kadan-kadan, yanzu gyaran motoci ya fara samuwa fiye da lokacin da aka janye tallafin man fetur a watan mayun 2023.
Abubakar Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, a ranar Alhamis, a lokacin da yake ƙarin haske kan alaƙar fara dawowar gyaran motoci dalilin raguwar farashin man fetur a Najeriya.
Ya ce a yanzu suna iya samun gyaran motoci a kalla guda ashirin a kowacce rana, saɓanin lokacin baya da idan sun je garejin sai dai su zauna babu gyaran, ƙarshe ma su koma gida ba tare da samun komai ba.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan yadda wasu ke ta kiraye-kiraye ga gwamnatocin Najeriya, kan su yi abinda ya dace don ganin al’umma sun samu sauƙi a al’amuran yau da kullum.

Labarai
Matashin da ke Sansana bayan Akuya yana sakawa a TikTok ya shiga hannun hukumar Hisbah a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani Matashi da aka yi zargin ya sansana bayan wata Akuya, a matsayin yana son ya yi suna a shafukan sada zumunta.
Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah Dakta Mujahideen Aminudeen Abubakar, ya shaidawa Dala FM Kano cewar, sun kama matashin ne mai suna Shamsu Yakubu dan garin Dawakin kudu, mai shekaru 24, bayan da dagacin garinsu ya kawo korafi akansa.
Dagacin ya ce an kai ƙorafin matashin ne saboda yadda mutanen garin suka yi kokarin farmasa, bayan da aka gano bidiyonsa a shafin TikTok yana sansana bayan Akuya.
Yanzu haka hukumar ta ɗauki matakin kai matashin a fara yi masa gwajin Ƙwaƙwalwa, da kuma na ta’ammali da kayan maye.

Labarai
Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.
Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.
Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.
A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su