Connect with us

Manyan Labarai

Tinubu ya san jam’iyya ta – Sanusi

Published

on

Jama’a mu kara riko da addini –Sarki Sanusi II

Yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, Mai martaba sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi na biyu, ya bayyana jam’iyya daya tilo da ya ke goyon baya a Najeriya.

Sanusi ya ce jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu na sane da cewa shi na jam’iyyar da ake kira Najeriya ne.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke cewa shi ba dan kowace jam’iyya ba ne.

Sanusi ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake zantawa da Tinubu da sauran baki a Kaduna a yayin bikin KadInvest karo na bakwai, wanda hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya a jiya.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, ya kuma koka da yadda ake satar mai, da karuwar basussukan da Najeriya ke fama da ita, rashin daidaiton biyan tallafin da ake samu da kuma hauhawar kudaden kasashen waje, da dai sauran kalubalen kudi da tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Ya yi kira da a yi gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da dukiyar kasa sannan kuma ya bukaci a kwancewa kamfanin man fetur na kasa (NNPC) Limited, yana mai cewa kamfanin ba saniya ba ce amma ya kamata a gudanar da shi a matsayin kamfani mai zaman kansa tare da bin diddigin al’amura.

Sanusi ya kuma bukaci Jihohin kasar da su ‘yantar da kansu daga dogaro da gwamnatin tarayya fiye da kima.

“Na ci gaba da maimaitawa, da fatan ku tuna cewa na rasa aiki a babban bankin kasa saboda wannan matsala.

“Ba batun wata jam’iyya ba ce. Bani da party. Jam’iyyata Najeriya ce. Wannan ita ce matsalar da muka samu a 2014. Asiwaju (Tinubu) ya san jam’iyyata ita ce Najeriya,” inji shi.

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta zargin gididdiba burtalai a wasu garuruwan ta uku

Published

on

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta batun gididdiba burtalai a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, dukka a ƙaramar hukumar da ake zargin an siyarwa Manoma, domin suyi aikin Noma.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan a daren jiya Laraba, lokacin da yake tsokaci kan koken da Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka yi, kan yadda suka zargi an gididdiba burtalai a yankunan su, an siyarwa wasu Manoma, domin suyi aikin Noma, lamarin da suka ce hakan barazana ce a gare su.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu wajen gididdiba burtalai a garuruwan, yana mai cewa ko da kansilolinsa daga zuwan su bai taɓa sanin wanda ya siyar da koda kuwa kunya ɗaya ba a cikin shugabancin sa na ƙaramar hukumar domin ayi Noma, haka shima bai siyar ba.

“Yanzu haka ana kan ɗaukar matakin doka akan waɗanda suka fitar da al’amarin, kasancewar maganar tana wajen ƴan sanda, kuma ana faɗaɗa bincike, “in ji shi”.

A ziyarar gani da Ido, da tashar Dala FM Kano, ta kai wasu daga cikin burtalan da aka yi zargin an siyarwa Manoman, ta iske yadda wasu mutane suke share guraren, kamar yadda suka shaida cewa waɗanda aka siyarwa ne suka basu aikin share wajen.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, wannan na zuwa ne bayan da wasu Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka koka, bisa yadda suka ce an gididdiba burtalai a yankunan su, duk da wani manomi yace har takarda aka bashi bayan an siyar masa, lamarin da ya sa su cikin damuwa bisa yadda hakan ka iya sanyawa su rasa guraren da za su yi kiwon Shanun su.

Continue Reading

Trending