Connect with us

Labarai

Labarai a Takaice na yau Litinin 06 05 2019

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da cigaban demokradiyya da samar da daidaito a zamantakewa SEDSAC, ta yi kira ga ‘yan kasuwa da su ji tsoron Allah wurin kaucewa Karin farashin kayan abinci a wannan lokaci na watan Azumin Ramadan.

Cikin wata takarda mai kunshe da sa hannun sakataran shirye-shiryen kungiyar, Kwamrade Abubkar MD Mukhtar ya sanyawa hannu, ta bukaci ‘yan kasuwa da su sassautawa al’ummar musulmai wajen ganin sun sami kayan abinci cikin sauki, haka zalika kungiyar ta kuma yi kira ga masu hannu da shunni dasu rinka tallafawa mabuka.

A ranar daya ga watan Ramadan ne Allah madaukakin sarki, ya aiko fiyayen halita a matsayin Annabi, kuma a wannan rana ce Annabi (SAW) ya fara ganin mala’ika Jibril a kogon Hira.

Haka zalika a wannan rana ce ta daya ga watan Ramadan, Annabi ya auri matar sa Zainab Bintu Khuzaima uwar miskinai, kuma wannan rana ce Annabi S.A.W ya fara yin sallar rokon ruwa.

Shugaban makarantar Zinatul Islam wa tahfizil kur’an dake Rafin Malam a karamar hukumar Ungogo, Ahmad Isma’il Ibrahim, ya yi kira ga daliban makarantar da su kiyaye kimar da Allah ya yi masu na hadace al’kurnai da su ka yi.

Ahmad Isma’il Ibrahim, ya yi wannan kiran ne yayin saukar daliban makarantar karo na farko da suka haddace al’kurani har su 14, inda ya kuma yabawa malaman makarantar bisa yadda suka jajirce wajan kula da karatun daliban.

Mataimakin kungiyar taimakon kai da kai wato ZUDA dake yankin unguwar Hausawa ta gidan Zoo, Usaini Haruna Kailu, ya bukaci masu hannu da shuni da ‘yan kasuwa da su rinka tallafawa marasa karfi a unguwannin su, musamman marayu.

Usaini Haruna Kailu, ya yi wannan kiran ne yayin rabon kayan abinci da kungiyar ta raba ga marayun yankin ciki akwai buhun shinkafa 145 da kuma katan din taliya 40.

Labarai

Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.

Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.

Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.

A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Continue Reading

Labarai

Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.

“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.

Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.

Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Continue Reading

Labarai

Za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 – Masani

Published

on

Wani masanin ilmin Taurari da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Mallam Nasir Falaki Al-Kanawi, ya ce za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 saboda watan Shawwal ba zai ganu ba a ranar Asabar, don da ƙarfe 11:58 na safe za a haifi jinjirin watan kuma zai faɗi 06:48 na Yamma.

Mallam Nasiru Alfaki Al-Kanawi ya bayyana hakan ne a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Juma’a 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.

Alfalaki ya kuma ce watan zai faɗi ne da ƙarfe 6:48 na yamma mintuna kasa da 10 kenan bayan faduwar Rana, kasancewar ranar ƙarfe 6:37 na yamma za ta fadi.

Ya ci gaba da cewa to wannan dalilin ne zai sa watan ba zai ganu ba, ko da kuwa da Na’ura ne kasancewar bai samu wadataccen hasken da zai ɗosana daga ranar ba, wanda aƙalla yana buƙatar awanni 13 zuwa 16 daga haifeshi kafin ace an iya ganinsa, Allah shi ne mafi sani Mai iko akan komai.

Continue Reading

Trending