Labarai
Rahoto: Za mu yi saukar Al-Qur’ani saboda matsalar tsaro da rikicin siyasa – Ibni Sina

Hukumar Hisba ta jihar Kano, ta shirya saukar Al-qur’ani mai gima guda dari biyar, saboda kaucewa faruwar rikicin siyasa da matsalar tsaro a Najeriya.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Muhammad Haruna Sani Ibni Sina, ya bayyana hakan, a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Ibrahim Abdullahi Soron Dinki.
Muna da cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Hangen Dala
Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.
“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.
Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Hangen Dala
An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.
A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.
Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.
Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Labarai
Gwamnatin Kano za ta Kara inganta aikin Jarida

Gwamnatin jihar kano tace za ta hada Kai da kungiyar ‘yan jarida masu magana a Radio da Television na kasa wato Society of Nigerian Broadcasters domin kara inganta aikin Jarida.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Baba Halilu Dan Tiye ne ya tabbatar da hakan lokacin da ake kaddamar da ‘ya’yan kungiyar anan kano.
Baba Halilu yace duba da muhimmancin da aikin jarida ke dashi a tsakanin al’umma ya sanya gwamnatin Kano za ta cigaba da baiwa bangaren muhimmanci.
Taron Wanda ya gudana a cibiyar ‘yan Jaridu ta Kano ya samu halartar Mafi yawa daga cikin shugabannin kafafen yada labaran Dake Kano.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano