Manyan Labarai
Za a yanke hukunci neman tsige Buhari da jam’iyyar HDP ta shigar da kara

Mai shari’a Inyang Edem Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a, ya sanya ranar 30 ga watan Janairun shekara mai zuwa, domin yanke hukunci kan karar da ke neman tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga mukaminsa da kuma dakatar da gudanar da zaben shugaban kasa na 2023.
Alkalin kotun ya sanya ranar yanke hukuncin ne biyo bayan amincewa da jawabin karshe da shugaba Buhari, da babban lauyan gwamnatin tarayya, da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kuma mai shigar da kara, Cif Ambrose Albert Owuru suka yi.
A zaman da aka yi ranar Juma’a, Cif Ambrose Albert Owuru, dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 a karkashin jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP), ya bukaci babbar kotun tarayya da ta dakatar da INEC daga gudanar da zaben shugaban kasa na 2023.
Ya yi wannan kiran ne bisa hujjar cewa, shi ne ya lashe zaben shugaban kasa a 2019 da kuma cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwace wa’adin mulkinsa.
Ya roki kotu da ta tsige Buhari ta kuma ayyana shi (Owuru) a matsayin ingantaccen shugaban kasa, sannan kuma a tursasa Buhari ya mayar da duk wasu kudaden da ya karba a matsayin albashi da kudaden alawus-alawus da na tsaro.
Owuru, ya kuma bukaci kotun ta ba da umarnin rantsar da shi na tsawon shekaru hudu bayan tsige Buhari daga mukaminsa.
Babban Lauyan ya bayyana wa kansa da Hope Democratic Party HDP sannan kuma ya ba da hujjar karshe.
Owuru da jam’iyyar HDP, sun kai karar shugaba Buhari da wasu mutane biyu suna neman kotu ta bayar da umarnin bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019.
Ya kuma yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben raba gardama da aka gudanar a shekarar 2019 kuma tun a wancan lokacin ne aka nada Buhari.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Labarai
Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.
Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano