Connect with us

Labarai

A na zargin magidanci ya azabtar da matarsa da yunwa na shekara guda

Published

on

An ceto wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Sadiya, bayan da mijinta ya tsare ta a gidansa har tsawon shekara daya ba tare da abinci ba a garin Nguru da ke jihar Yobe.

A cewar Daily Post, Aisha mai ‘ya’ya hudu ‘yar jihar Kano ce, wadda mahaifiyar ta Hadiza, ta ceto ‘yarta ta daga mawuyacin hali a makon jiya.

Wata majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaye sunanta ta ce, “Mahaifiyar ta yi tattaki zuwa Nguru daga Kano, domin ganin diyarta a lokacin da ta ji rashin jin dadin muryarta a waya, amma sai ta hadu da ita a wani yanayi na kusa da mutuwa, bayan da yunwa da sauran cututtuka su ka yi mata lahani.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa, an garzaya da Sadiya zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke Kano, inda a halin yanzu take jinya tare da mahaifiyarta ta na neman a hukunta surukarta, wanda a cewarta ya lalata rayuwar diyarta.

Ta kuma yi kira ga gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da ya sa baki.

Labarai

Kisan gillar Edo: A gaggauta nemawa mutanen da aka kashe haƙƙin su, ko mu ɗauki Mataki bisa doka – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Rights Network, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Kano da kuma ta jihar Edo, da gaggauta neman haƙƙin Mafarautan nan ƴan asalin jihar Kano waɗanda aka yi wa kisan gilla a garin Uromi na jihar Edo.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Gambo Madaki shi ne ya bayyana wa tashar Dala FM Kano, hakan a ranar Litinin, lokacin da yake tsokaci kan kisan sama da Mafarauta 16 a jihar Edo, waɗanda suka taho daga jihar Ribas za su dawo gida Kano.

Ya ce baya ga ɗaukar matakin lalubo waɗanda suka aikata rashin imanin, akwai buƙatar a ɗauki mummunan mataki akan su don daƙile afkuwar irin hakan a gaba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓatabgari ne su ka damke wadanda abin ya shafa a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta Jihar Edo, inda su ka ga bindigogin farauta, sai kawai su ka yanke cewa ai masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu a ranar Alhamis.

Lamarin dai ya jawo cece-ku-ce, inda ‘yan Najeriya da dama ke zargin gwamnati da gazawa wajen dakile irin wannan ɗaukar doka a hannu.

A cewar Gambo Madaki, baya ga batun kafa kwamiti da gwamnatin Kano ta yi akan wannan batun, ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara bibiyar lamarin da kan sa, don ganin an ɗauki matakin da ya dace akan kisan gillar ko kuma su ɗauki mataki bisa doka.

Continue Reading

Labarai

Mun baza jami’an mu lungu da saƙo don samar da tsaro yayin bikin Sallah a Kano – Anty Snaching Phone

Published

on

Rundunar tsaron nan da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma dakile Shaye-shayen kayan maye, ta Anty Snaching Phone, ta ce ta baza jami’an ta kusan dubu ɗaya da za su shiga lungu da saƙo na jihar nan, domin samar da tsaro a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Kwamandan rundunar a nan Kano Inuwa Salisu Sharaɗa ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen daƙile ayyukan ɓata garin da ke shirin tayar da hankalin al’umma yayin bikin sallar.

“Daga cikin jami’an mu da za su samar da tsaron akwai na cikin kayan mu da kuma na farin kaya, kuma sun fara bazama guraren da mu ka tura su tun cikin kin daren Asabar ɗin nan kuma za su yi aiki cikin ƙwarewa kamar yadda suka samu horo, “in ji Inuwa”.

Sharaɗa, ya kuma ce hakan na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da miyagun ɗabi’u da gwamnan ya kafa ƙarkashin Dakta Yusuf Ƙofar Mata.

Wannan dai na zuwa ne yayin da za’a gudanar da sallar Idi, ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadin nan a Najeriya, da Jamhuriyyar Nijar da ƙasar Saudiyya, da ma wasu ƙasashen Duniya.

Continue Reading

Labarai

Za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 – Masani

Published

on

Wani masanin ilmin Taurari da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, Mallam Nasir Falaki Al-Kanawi, ya ce za a cika Azumin Ramadan na shekarar 1446 guda 30 saboda watan Shawwal ba zai ganu ba a ranar Asabar, don da ƙarfe 11:58 na safe za a haifi jinjirin watan kuma zai faɗi 06:48 na Yamma.

Mallam Nasiru Alfaki Al-Kanawi ya bayyana hakan ne a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi wa gidan rediyon Dala FM Kano a ranar Juma’a 28 ga watan Maris ɗin shekarar 2025.

Alfalaki ya kuma ce watan zai faɗi ne da ƙarfe 6:48 na yamma mintuna kasa da 10 kenan bayan faduwar Rana, kasancewar ranar ƙarfe 6:37 na yamma za ta fadi.

Ya ci gaba da cewa to wannan dalilin ne zai sa watan ba zai ganu ba, ko da kuwa da Na’ura ne kasancewar bai samu wadataccen hasken da zai ɗosana daga ranar ba, wanda aƙalla yana buƙatar awanni 13 zuwa 16 daga haifeshi kafin ace an iya ganinsa, Allah shi ne mafi sani Mai iko akan komai.

Continue Reading

Trending