Connect with us

Labarai

Gwamnati za ta kashe masarautar Kano- Farfesa Naniya

Published

on

Wani Malami dake sashen tarihi a jami’ar Bayero dake nan Kano, Farfesa Muhammad Tijjani Naniya, ya ce shirye-shiryen da gwamnatin jihar Kano ke yin a samar da Sarakunan Yanka illa kawai koma baya ga masarautar Kano.

Farfesa Naniya, ya bayyana hakan ne ya yin zantawarsa da gidan rediyon Dala, ya na mai cewa, abin da gwamnati ke yi abune da zai jawowa jihar Kano koma baya musamman ma ta bangaren masarauta.

Ya kuma ce hakan zai haifar da rarrabuwar kawunan sarakunan maimakon hada kansu kuma hakan zai iya rage dandazon baki da suke zuwa kallon hawan Sarki a Kano duba da yadda Sarakunan za su kasu kashi-kashi.

 

Labarai

Gwamnatin Kano ta nemi matasa su nemi ilimin aure kafin yin sa

Published

on

Daraktar kula da al’amuran mata a ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Kano, Hajiya Kubura Ibrahim Dan Kani, ta yi kira ga mata da maza masu shirin yin aure dasu kasance masu ilimin aure kafin yin sa.

Hajiya Kubra, ta bayyana hakan a zantawar ta da gidan rediyon Dala yau Talata.

Ta ce” Maza da mata su nemi ilimin zamantakewar aure kafin su yi aure sakamakon sabani da ake samu domin wasu ma’auratan ba su san me ne auren ba, kawai suna yi ne auran kai tsaye ba tare da sun san muhimmancin sa ba. Kuma mun shirya tsaf a yanzu domin wayar da kan wasu daga cikin maza da mata masu shirin yin aure domin basu bita ta musamman a kan auratayya”. A cewar Kubura.

Sannan kuma hukumar mu tan a tallafawa marayu da marasa galihu a birni da karkara ta hanyar koya masu sana’o’in dogaro da kai, kuma duk wani mai bukatar hakan kofar mu a bude ta ke wajen tallafa masa”. Inji Kubura.

Wakilin mu Nasir Kalid Abubakar,ya rawaito cewa daraktar hukumar a shirye suke da su bada tallafi ga masu bukatar hakan, musamman a bangaren koya mu su sana’o’in dogaro da kai tare da zamantakewar aure.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

An tono wata gawa da aka bunne a Kano

Published

on

Tun da fari dai Babbar kotun shari’ar Muslunci ce mai zaman ta a  kofar Kudu ce karkashin mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, ta yi umarnin a yiwa gawar sutura kasancewar hukumar Hizba ta roki kutun ta yiwa asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano Umarnin su bayar da gawar wani mai suna, Abdullahi Obinwa, inda a nan ne aka samu akasi aka musanya gawar da ta wani dan kabilar Ibo mai suna Basil Ejensi, bayan kuma ya cika umarnin kotun da kwanaki bakwai da binne shi.

Sai dai wasu ‘yan kabilar Ibo suka garzaya kotun ta mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, suka yi roko a gaban kotun cewar anyi musu musayar gawa domin haka kotun ta yi umarni a kwakulo gawar da ta bayar da damar binewa kwani bakwai da suka gabata domin dai tasu ce bata wadanda suka nema ba tun da fari.

Bayan jin kowanne bangare mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, ya bayar da wani umarnin cewar a samu rakiyar jami’an tsaro zuwa makabartar domin tono gawar mai kwanaki bakwai a bunne ta a waccan makabartar ta unguwar Gandun Albasa dake Karamar Hukumar Birnin Kano, da yammacin ranar Litinin dinnan,

Harma bayan kwakulo gawar daga kabarinta ankuma damkata ga Lauyan gawar Masalinas Duru, harma lauyan ke cewa” Hukuncin kotun ya yi mana dadi sakamakon an bamu gawar mu”.

Shima limamin da ya sallaci gawar Malam Aminu Ahmad Adam, ya ce” Kuskure ne an riga an yi shi kuma babu wanda ya wuce ya aikata shi”.

Sai dai Jami’in hukumar Hizba mai lura da Makabarta, Malam Jamilu, wanda su ne suka yi kara ta farko ya ce” Na yi mamaki  game da wannan lamarin da ya kasance”.

Suma wasu da suka ganewa Idanuwansu yadda Ka hako gawar sunce har da jami’an tsaro a rakiyar kuma a gaban su aka kwakulo gawar sannan aka daura shi a gadon asibiti kuma tuni ‘yan uwan sa suka tafi da shi.

Continue Reading

Labarai

Muna dab da rufe rijistar baburan Adaidaita sawu -KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano, (KAROTA), ta ce za ta rufe yin aikin rijistar babura masu kafa uku wato adaidaita sahu a ranar Laraba mai zuwa.

Shugaban hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ne ya tabbatar da hakan a wata ganawa da ya yi da shugabannin kungiyar ‘yan Babura masu taya uku a yau Lititinin.

Ya ce” In Allah ya yarda a ranar Labara idan an rufe dole ne ya ajiye babur din sa sakamakon bas hi da lambar rijista a babur din sa saboda dazarar mun gan shi to ya karya doka”.

Ya kuma ce” Sannan ina sanar da masu baburan da su tabbata sun yi rijistar kafin ranar domin gudun haduwa damu ”. inji Baffa

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish