Connect with us

Labarai

Ƴan sanda sun kama ƴan Jaridar bogi a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wasu ƴan jaridar Bogi da suka yi yunƙurin cuta a wani katafaren shago dake jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan, a cikin shirin Ɗan sanda Abokin Kowa, na tashar Freedom Radio, a ranar Lahadi.

Ya ce, Mutanen sun je katafaren shagon ne dake kan titin BUK, inda suka sayi Shinkafa ta Naira dubu 33 tare da turawa masu kayan sauƙon kuɗi na bogi, wato Feck Alert”.

“Bayan da jami’an mu na sharaɗa ƙarƙashin Baturen ƴan sandan Sharaɗan SP Abdulraheem Adamu suka samu kiran gaggawa ne, suka garzaya tare da kama mutumin daga bisani kuma suka kama abokin aikin jaridar bogin nasa,”. Inji Kiyawa.

Kuma bayan an kama mutanen ne aka garzaya gidan rediyon Vision da mutanen suka ce a can suke aiki, inda gidan rediyon suka ce ba ma’aikatan su ba ne, daman ɗaya yayi musu laifi ne ya tafi da ID Card ɗin su yaje aka sanya sunansa a jiki amma ba Ma’aikacin su ba ne.

Wamilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, SP Kiyawa ya ce yanzu haka Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Mamman Dauda ya bayar da umarnin idan ƴan sandan su na Sharaɗa sun kammala bincikensu, za’a mayar da mutanen babban sashin binciken manyan laifuka dake Bompai, don ɗaukar matakin kai su kotu kan zargin da ake musu.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending