Connect with us

Manyan Labarai

Za a fitar da sabon mafi kankantar albashi na 2024 ._Chris Ngige

Published

on

Kungiyar kwadago

Ministan kwadago da Ayyuka Chris Ngige, ya ce an kammala komai domin samar da sabon tsarin mafi kankantar albshi a kasar  nan daga watan Mayu na 2024.

Ministan wanda ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar a Abuja, wajen taron wakilai na kasa karo na 13 na kungiyar Kwadago ta NLC, ya kuma gargadi kungiyar da sauran takwarorinta na kwadago kan su daina shiga sha’anin gwamnati da kokarin tilastawa gwamnati ra’ayinsu a kan abubuwan da suka shafi nadin mukamai.

Ngige ya zargi kungiyoyin kwadago da saba dokar da ta kafa su, wadda ta zartar da cewa dole ne duk sabbin shugabannin da aka zaba su halarci bitar sanin makamar aikinsu a Cibiyar Nazarin Harkokin Kwadago ta Kasa ta Michael Imuodu.

Ministan ya ce samun wannan horo zai sa shugabannin kwadago su samu ilimi da kwarewar da ta dace ta yadda za su zama kwararru a harkar mu’amulla ta kwadago.

NLC zanga-zanga Kano: Ba makaranta ba zaben 2023 – Dalibai

Chris yace a yanzu sun sanya dokar da ta tanadi cewa duk bayan shekara biyar wajibi ne a sake bibiyar tsarin da ake amfani da shi kan mafi kankantar albashi, wanda a yanzu ke nan dole ne Najeriya ta samar da sabon tsarin mafi kankantar albashi nan da watan Mayu na 2024.

Manyan Labarai

Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Published

on

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.

” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.

Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.

Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya fara rusau

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara rushe wasu gine gine da aka yi su a wuraren gwamnati Ba bisa ka’ida ba.

A cikin daren Asabar din nan ne tawagar Kwamitin kar ta kwana mai lura da rushe gine gine ta fara da rushe wani sabon rukunin shaguna mai kunshe da sama da shaguna 90 dake jikin filin sukuwa a jihar Kano.

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewar wannan aiki somin tabi ne domin batun rushe gine ginen da aka yi su akan filayen jama ar Kano lamari ne da babu gudu babu ja da baya kamar yadda gwamna Engr Abba Kabir Yusif ya bayyana a lokacin da yake yakin neman zabe.

Tawagar kwamitin na kar ta kwana zai cigaba da rushe dukkan wasu gine gine da aka yi su ba bisa kaida ba.

Continue Reading

Trending