Connect with us

Manyan Labarai

Kotu ta aike da Alasan Ado Doguwa gidan Gyaran hali

Published

on

Kotun majistret mai lamba 54 karkashin mia shari’a Mansur Ibrahim Yola ta aike da hon Alhassan Ado Doguwa gidan gyaran hali.

Yansanda ne dai suka gurfanar da Alhassan Ado bisa zargin hada baki dayar da hankalin al’umma, haddasa gobara, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma laifin kisan kai.

Kunshin zargin ya bayyana cewar Alhasan Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar tarayyar Najeriya ya hada baki da wasu mutane sun tayar da hankalin al’umma a yankin Tudunwada da Doguwa a yayin gudanar da babban zabe wanda ya gabata makon da ya gabata.

Kunshin zargin ya bayyana cewar bayan samun sa da miyagun makamai an kuma zargi Alhassan Ado da laifin tayar da gobara da jikkata mutane da kuma laifin kisan kai .

Jim kadan bayan kammala karanta zarge-zargen lauyan Alhassan ya roki a sanya shi a hannun beli

Sai dai lauyan gwamnati yayi suka bayan musayar yawu tsakanin masu gabatar da kara da lauyoyin kariya karshe dai mai shari,a ya tisa keyar Alhassan zuwa gidan gyaran hali.

An kuma ayyana ranar 7 ga watan gobe dan a kara gabatar da shi

Labarai

Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.

Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.

Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Published

on

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.

Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.

” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

 

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Published

on

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.

Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.

Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Continue Reading

Trending