Manyan Labarai
Ganduje na kawo cikas a sha’anin Mika Mulki – NNPP

Jam’iyyar NNPP mai jiran gado a Kano ta zargi gwamnatin jihar mai barin gado da yin zagon ƙasa ga shirin miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.
A wani taron manema labarai a ranar Juma’a, shugaban kwamitin miƙa mulki na gwamna a jam’iyyar NNPP Dr Abdullahi Baffa Bichi ya yi zargin cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, da gangan tana kawo cikas ga shirin miƙa mulki.
Ya ce gwamnatin ta bai wa jam’iyyar NNPP gurbi uku kawai a cikin kwamitin da aka kafa don miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.
Bayan zaɓen 18 ga watan Mairis ne aka bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano, inda ya kayar da ɗan takarar jam’iyya mai ci ta APC a ƙarkashin gwamna Abdullahi Ganduje.
Dr Baffa Bichi ya ce “mutanen jihar Kano sun cancanci samun shirin miƙa mulki da zai tafi salin alin ba tare da tangarɗa ba.”
Ya ce ba su amince da tsarin da gwamnatin ta gabatar musu na cewa ɓangarenta ne zai kawo kashi 82 na ‘yan kwamitin miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati ba.
Sai dai har zuwa yanzu ba a ji wani abu daga gwamnati mai barin gado ba, kan zargin da jam’iyya mai jiran gado ta yi a kanta ba.

Manyan Labarai
DSS sun kama Emefele bayan dakatar dashi daga Gwamnan banki

Rahotanni na cewa jami’an tsaro na farin kaya DSS sunyi awon gaba da Godwin Emefele, sa’a guda bayan Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya dakatar dashi daga Gwamnan babban banki.
Tun abaya dai an zargi Emefele da hannu wajen gurgunta tattalin arzikin kasa, baya ga zargin sa, da hannu wajen tabarbarewar tsaro.

Manyan Labarai
Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.
Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.
” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.
Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.
Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Manyan Labarai
Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano