Connect with us

Manyan Labarai

Zamu hukunta duk Wanda aka samu da laifi – NNPP

Published

on

Jam’iyyar NNPPn Kano, ta zargi gwamnatin APC karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da sayar da wasu kadarori mallakin gwamnatin jihar.

 

Zargin wanda ake kallon gwamnatin jihar na siyar da kadarorin ga dan gwamna ba bisa ka’ida ba, abin da Jami’ar ta NNPP tace ba zata lamunta ba.

 

Har ma jami’iyyar ta ce za tayi bincike da tabbatar da hukunci da zarar sun karbi mulkin Kano a ranar 29 ga watan Mayu.

 

Jawabin hakan na zuwa ne ta bakin shugaban kwamitin karbar mulkin jihar Kano na jam’iyyar NNPP Abdullahi Baffa Bichi, yayin wata ziyara da yakai Hukumar Kano State Public Procurement Bureau a yammacin wannan Larabar.

 

Zargin da ke nuna cewa hukumar na cikin kadarorin gwamnati da aka siyarwa da dan gidan gwamna, akan kudi kimanin Miliyan 10, duk da cewa darajar hukumar ta kai Miliyan 50, a cewarsa.

Har ya zuwa yanzu dai gwamnatin Kano ba tayi martani game da zargin ba.

Manyan Labarai

Mun wayi gari da ganin gawar wani Matashi a Tunga ɗauke da Mukullaye da Filaya – Gamayyar matasan Kano

Published

on

Al’ummar unguwar Tunga da ke yankin Ɗorayi a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano, sun shiga ruɗani bisa yadda suka wayi gari da ganin gawar wani matashi ɗauke da wasu Mukullaye da Filaya a tare dashi, wanda ba a san daga inda yake ba.

Shugaban ƙungiyar da ke rajin kare haƙƙin Matasa da wayar da kan su a kan illar faɗan Daba da fashin Waya da Shaye-shayen kayan maye ta Gamayyar matasan Kano Muhammad Tajjani Ɗorayi, shi ne ya bayyanawa Dala FM hakan a cikin daren Laraba 09 ga watan Yulin 2025.

Ya ce marigayin da ba’a kai ga gano ƴan uwan sa ba, tuni jami’an tsaro suka kai shi asibiti, don yin abinda ya dace akan lamarin.

MTD, ya ƙara da cewa Marigayin matashin yana sanye da wandon Shadda, da ƙaramar Riga a jikinsa, a lokacin da aka ga gawar tasa a yankin Tunga da ke yankin Ɗorayi a Kano.

“Marigayin har zuwa ranar Laraba ba a samu wanda ya zo ya ce ɗan uwansa ne ba, duk wanda ya nemi ɗan uwansa mai kamanceceniyar matashin zai iya zuwa Ofishin ƴan Sanda na Kuntau a Kano, domin ƙarin bayani, in ji shi”.

Muhammad Tajjani ya kuma yi kira ga iyaye da hukumomi, da su ƙara jan matasa a jiki tare da samar musu abubuwan yi ta yadda za a cire musu sha’awar harkokin faɗan Daba da fashin Waya da Makami, la’akari da cewar idan matasan suna da abin yi ba lallai su rinƙa sha’awar aikata irin waɗancan miyagun ayyukan ba.

Tajjani Ɗorayi, ya kuma shawarci matasan da suke da irin ɗabi’ar aikata miyagun ayyuka suke damun jama’a a sassan jihar nan, da su daina su rungumi sana’o’i komai ƙankantar su, don ganin sun dogara da kan su, gami da zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamna Abba Kabir ya amince da naɗa Dr. Sulaiman Wali Sani a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗa Dr. Suleiman Wali Sani, a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Kano.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai babban daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikewa manema labarai a ranar Alhamis 10 ga watan Yulin 2025.

Dr. Sani, ƙwararren likita ne, kuma masani a harkokin yau da kullum, sannan tsohon babban Sakataren Gwamnati, wanda ke da sama da shekaru arba’in yana hidimata wa al’umma a ma’aikatun gwamnati.

Kafin wannan sabon naɗin dai, Dr. Sani ya kasance mai Baiwa Gwamna Shawara Kan Harkokin Ma’aikata.

Ya kammala karatun likitanci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digirin MB, BS, haka kuma, ya samu difloma daga Jami’ar Bayero da takardar shaidar mni daga Cibiyar Nazarin Harkokin Tsare-Tsare da Dabaru ta Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru.

Dr. Sani ya rike mukamai da dama masu muhimmanci, ciki har da Darakta Janar a ma’aikatun lafiya da kasuwanci, Sakataren Zartarwa, da Babban Sakataren Gwamnati a hukumomin jihar.

Haka zalika, ya shugabanci manyan asibitoci na jihar irin su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, da na Muhammad Abdullahi Wase.

A wani ci gaban kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa tsohon babban jami’in soji da ya shafe sama da shekaru 35 a rundunar Soja, Manjo Janar Mohammed Sani mai ritaya, a matsayin sabon babbban Darakta Janar na ayyuka na musamman a gidan gwamnatin Kano.

Sanarwar ta kuma ce waɗanda aka naɗa ɗin za su fara aiki ne nan take, inda gwamnan ya taya su murna bisa sabbin matsayin da aka naɗa su.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun kama mutane 98 da zargin miyagun Laifuka daban-daban a Kano – Ƴan Sanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana kama aƙalla mutane 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da bayyana wasu kayayyakin da aka samu nasarar kwato su a hannunsu kuma ciki har da Babura da Adai-daita Sahu da kayan maye da dai sauransu.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Ibrahim Adamu Bakori, ne ya jagoranci holen mutanen da ma kayayyakin ranar Alhamis, a shalkwatar rundunar da ke Bompai.

Ya ce cikin waɗanda aka kama akwai mutum 21 da ake zargi da garkuwa da mutane, da mutune 12 da zargin satar mota, sai mutane 8 da zargin satar Shanu, da kuma mutane 4 da ake zarginsu da fyaɗe, inda kuma mutane 5 ake zargin su da safarar Makamai, sai kuma mutane 47 da ake zargi da harkokin Daba a jihar Kano.

Kazalika, rundunar ta bayyana wasu muhimman kayayyakin da ta kama da suka haɗa da motoci guda 6, da Babura masu ƙafa biyu 8, da bindigogi ƙirar gida 13, sai kuma Wuƙake guda 98, da tabar Wiwi guda 35, da kuma ƙananan daurin tabar wiwin guda 1,123, da ƙwayoyi masu haɗari irin su Madarar Suck and Die, da Kwayar Exol, sai kuma D5, da Diazepam fiye da guda 150, da kuma kuɗin ƙasar waje har Dala $10,000.

Kwamishinan ƴan sandan Bakori, ya kuma ce nasarorin sun biyo bayan sabbin dabarun da rundunar ke amfani da su karkashin shirin Operation Kukan Kura, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi da al’ummar gari.

Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai tare da bayar da bayanan sirri domin ci gaba da yaƙar miyagun laifuka a faɗin jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Trending