Connect with us

Wasanni

West ham united ta lashe kofin conference

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta West Ham United ta yi nasarar lashe gasar Europa Conference na nahiyar turai, bayan doke kungiyar kwallon kafa ta Piorentina da ci biyu da daya.

Dan wasan kungiyar West Ham Benrahma ne ya fara zura kwallo a minti na 62, daga bisani dan wasan Piorentina Benoventure ya farke kwallon a minti na 67,gab da tashi daga wasan dan wasa Bowen ya tasa West Ham a gaba a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 90, inda aka tashi kwallon kungiyar kwallon kafa ta Piorentina na da kwallo daya West Ham United na da kwallo biyu.

Tin a shekarar 1980 rabon da kungiyar kwallon kafa ta West Ham ta lashe wani kofi, shekaru 43 kenan.

West Ham dai, itace kungiya ta biyu da ta lashe gasar ta Europa Conference a tarihi, bayan kungiyar kwallon kafa ta Roma da ta fara lashe gasar a karon farko a kakar shekarar 2021 zuwa 2022.

Wasanni

Kano Pillars ta sayi Salisu Abdullahi

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Capital City da take a babban birnin tarayya Abuja wato Salisu Abdullahi

Salisu ya rattaba kwantaragin shekara daya da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuru tare da yan wasan kungiyar, dan ganin kungiyar ta samu nasarori a gasar da zata buga ta cin kofin kwararru na Nigeria ta shekarar 2023 zuwa 2024.

Continue Reading

Wasanni

Chelsea ta sayi Lavia daga Southampton

Published

on

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Southampton wato Romeo Lavia a kan kudi €58m.

Romeo Lavia, dan asalin kasar Belgium mai shekaru 19, ya rattaba kwantaragin shekaru bakwai da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

Kafin komawar dan wasa Lavia kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton wasanni 34.

“Ina farin cikin komawa ta kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kuma komawar ta zo min kamar a mafarki, domin Chelsea kungiya ce da take da tarihi kuma kowanne dan wasa zai so ace yana buga wasa a Chelsea, kuma zan hada kai da abokan wasana dan ganin mun kai kungiyar mu ga babban mataki” a cewar Lavia.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta dauki sabbin yan wasa

Published

on

A yunkurinta na tunkarar sabuwar kakar wasan gasar Firimiyar Nigeria wato NPFL ta shekarar 2023 zuwa 2024, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sayi sabbin yan wasa guda uku domin yin garan bawul ga kungiyar.

‘Yan wasan dai sun hadar da Ibrahim Mustafah Yuga da Abubakar Ibrahim Babawo wayanda suka tawo daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Plateau United dake jihar Jos, sai kuma Abubakar Aliyu daga Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists dake jihar Bauchi, sanarwar dai ta fito ta hannun mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa.

Continue Reading

Trending