Connect with us

Manyan Labarai

An kaddamar da aikin tantance masu kwashe shara a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace ta kaddamar da aikin tantance ma’aikatan hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan ne domin gano bara gurbi da gano matsalolin wasu daga cikin ma’aikatan suke fuskanta domin inganta ayyukansu.

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano Honourable Nasiru Sule Garo ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddanar da aikin tantance ma’aikatan a hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan.

Garo yace duba da yadda koke suka yi yawa daga cikin ma’aikatan hukumar musamman kanana ma’aikatarsa taga dacewar ayi na musamman tare da yin garanbawul domin samun cikakkiyar nasarar ayyukan Ma’aikatar.

Da yake jawabi tun da farko tsohon shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Injiniya Abdullahi Shehu Wanda shine shugaban kwamitin tantance ma’aikatan, ya bukaci hadin kan ‘yan kwamitin nasa domin gudanar da aikin cikin nasara.

Daga karshe kwamishinan Ma’aikatar Muhallin ta jihar Honourable Nasiru Sule Garo yace kwamitin zai yi aikinsa cikin kwanaki 5 tare da Mika rahotonsa.

Manyan Labarai

Fadan dabar kofar Na’isa da kofar Dan-agundi, laifin iyaye – Mazaunin Yankin

Published

on

Wani mazaunin ƙofar Na’isa wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce faɗan dabar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin da Ɗan Agundi, laifin iyaye ne, da kuma wasu manya a unguwannin da ake zargin suna goya musu baya ta hanyar daƙile yunƙurin hukumomi na ɗaukar doka a kansu.

Mutumin ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, biyo bayan yadda rikicin faɗan dabar ya sake ɓarkewa a unguwannin a Alhamis ɗin nan, al’amarin da ya janyo asarar dukiyoyin al’umma a yankunan.

Ya ce lamarin ya faro ne tun a lokacin bikin ƙaramar Sallah, lamarin da a baya ƙura ta lafa, sai dai kuma a ranar Alhamis ɗin sai gashi an sake samun faɗan dabar.

A cewar sa, “A lokacin faɗan dabar ya faru an Sassari mutane da dama, hatta Saniya ma ba ta tsira ba sai da aka sareta, tare da fasa gilasan ababen hawan Mutane, “in ji shi”.

Sa dai mutumin ya ce, tuni jami’an tsaron Ƴan Sanda, suka kai ɗauki tare da kwantar da tarzoma, lamarin da ƙurar ta lafa.



Continue Reading

Manyan Labarai

Ba za mu amince da yadda ake yawan kai wa jami’an mu hari ba a Kano – KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirgar-zirgar ababen Hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta ce ba za ta lamunta da yadda ake yawan kai wa jami’anta farmaki ba, na ba gaira babu dalili yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Shugaban Hukumar KAROTA, a Kano, Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya yi wannan gargaɗin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya aikowa tashar Dala FM Kano, a ranar Laraba 09 ga watan Afrilun 2025.

“Hakan na zuwa ne biyo bayan wani mummunan hari da wasu mutane da ke cikin baburin Adai-daita sahu suka kai wa jami’an na mu yayin da suke tsaka da aikinsu a titin da ke dab da gidan Buhari kan hanyar zuwa Gidan Zoo, “in ji shi“.

Sanarwar ta ce, tunda farko an tsayar da wani mai baburin Adai-daita Sahu ne inda yaƙi tsayawa, sai kawai aka hango mai ɗan sahun ya naushi jami’in karotar.

Sai dai a ta bakin Shugaban kungiyar ‘Yan Adai-daita Sahu a jihar Kano, ya ce waɗannan mutane ba halattattun ‘Yan Adai-daita Sahu ba ne, sun dai fake da sana’ar su dan aikata ta’addanci.

Daga bisani dai jami’n hulɗa da jama’a na Hukumar Koratar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya ce hukumar za ta ɗauki tsattsauran mataki akan lamarin, don kare afkuwar irin hakan a gaba.

Hukumar ta ce duk wanda ya ga faruwar wani abu da ya shafe ta, ko kuma ƙorafe-ƙorafe, zai iya kiran waɗannan lambobin domin sanar da ita, da suka haɗar da 09015709449 ko 08059689422 ko kuma 08067311520.



Continue Reading

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.



Continue Reading

Trending