Connect with us

Manyan Labarai

Dalilin majalisa na kin amincewa da El Rufa’i a matsayin Minista

Published

on

Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da sunayen mutum 45 daga cikin 48 da Shugaban kasa Bola Tinubu ya aike mata don amincewa da naɗa su minista.

Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya karanto sunayen da majalisar ta tantance ɗaya bayan ɗaya, yayin da sauran ƴan majalisar suka riƙa amsa tambayar amincewa ko akasin hakan.

Ga jerin sunayen waɗanda aka tabbatar a matsayin ministoci:

Abubakar Momoh – Edo

Betta Edu – Kuros Riba

Uche Nnaji – Enugu

Joseph Utsev – Binuwai

Hannatu Musawa – Katsina

Nkeiruka Chidubem Onyejocha – Abiya

Stella Okotete – Delta

Uju Kennedy-Ohanenye – Anambra

Ahmed Dangiwa – Katsina

Olawale Edun – Ogun

Imaan Suleman Ibrahim – Nasarawa

Bello Muhammad Goronyo – Sokoto

Nyesom Wike – Ribas

David Umahi – Ebonyi

Mohammad Badaru Abubakar – Jigawa

Lateef Fagbemi – Kwara

Doris Aniche Uzoka – Imo

Yusuf Maitama Tuggar – Bauchi

Farfesa Ali Pate – Bauchi

Ekerikpe Ekpo – Akwa Ibom

Mohammed Idris – Neja

Olubunmi Tunji Ojo – Ondo

Dele Alake – Ekiti

Waheed Adebayo Adelabu – Oyo

John Eno – Kuros Riba

Abubakar Kyari – Borno

Abdullahi Tijjani Gwarzo – Kano

Dr Mariya Bunkure – Kano

Ishak Salako – Ogun

Bosun Tijjani – Ogun

Tunji Alausa – Legas

Tanko Sununu – Kebbi

Adegboyega Oyetola – Osun

Atiku Bagudu – Kebbi

Bello Matawalle – Zamfara

Ibrahim Geidam – Yobe

Simon Lalong – Filato

Lola Adejo – Legas

Shuaibu Abubakar – Kogi

Tahir Mamman – Adamawa

Aliyu Sabi Abdullahi – Neja

Alkali Ahmed Saidu – Gombe

Heneken Lakpobiri – Bayelsa

Uba Maigari – Taraba

Zephaniah Jissalo – Abuja

Sauran mutum uku da majalisar ba ta tabbatar da nadinsu ba su ne:

Nasir El-Rufai – Kaduna

Sani Abubakar Danladi – Taraba

Stella Okotete – Delta

majalisar tace dukkanin ukun har yanzu hukumomin tsaro Basu kammala bincike a kansu ba.

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta nemi ƴan sanda su fitar da Aminu Ado Bayero daga gidan sarki na Nassarawa

Published

on

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya nemi ƴan sanda su fitar da Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, daga cikin gidan Sarki na Nassarawa, daga yanzu zuwa kowanne lokaci.

Kwamishinan Shari’a na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da yake gudanarwa yanzu haka a gidan gwamnatin jihar Kano, kamar yadda Dala FM ta rawaito.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya dake Gyaɗi-gyaɗi a Kano, ta yanke a yau, inda ta soke naɗin da gwamnatin Kano ta yiwa Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin sarkin Kano, amma ta ce dokar da majalisar dokokin jihar ta yiwa kwaskwarima na zata ce komai akai ba, kasancewar bata da hurumi akai.

Aminu Babba Ɗan Agundi ne dai ya yi ƙarar gwamnatin jihar Kano, da majalisar dokokin jihar yana ƙalubalantar rushe masarautun da tayi, lamarin da ya ce an tauye masa haƙƙi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotu tayi hukunci akan masarautar Kano

Published

on

Babbar kotun tarayya mai zaman ta a Gyadi-gyadi da ke jihar Kano, ta bayyana matsayarta akan a karar da Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar

gabanta akan batun rushe dokar masarautu ta shekarar 2019.

Tun da garko mai kara Aminu Babba Dan Agundi ya yi karar gwamnatin jihar Kano, da majalisar dokokin jihar Kano, inda ya bayyanawa kotun cewar rushe dokar da majalisa ta yi an tauye masa hakkin sa.

Sai dai lauyoyin waɗanda akayi karar sun bayyana wa kotun cewar Aminu Babba Dan Agundi, bashi da wani hakki da majalisar ta tauye masa, sun kuma bayyanawa kotun cewar bata da hurumin sauraron shari’ar masarautu dan haka suka roki kotun da ta yi watsi da karar.

Yayin da ya ke bayyana matsayar sa a yau Alhamis, mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya ce ya soke nadin da akayi wa Muhammadu Sunusi
na biyu, amma hakan bai shafi dokar da majalisar ta yi wa gyaran fuska ba
domin kotun bata da hurumi a kanta.

Kotun ta kuma ce za ta tsaya iya haka har sai kotun ɗaukakar da gwamnatin jihar Kano ta shigar ta gama nata, duk kuwa da a baya Alƙali Liman ya ce ba zai dakata ba tunda bai samu umarni daga kotun ɗaukaka ƙarar ba.

A yayin zaman shari’ar dai an girke jami’an tsaro a yankin Gyaɗi-gyaɗi da babbar kotun tarayyar take zaune domin samar da tsaro.

Wakilinmu na Kotu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, mai shari’a Liman ya kuma ayyana cewar umarnin da ya bayar tun da farko na cewar kowa ya tsaya a inda yake yana nan bai janye shi ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun kama mutum ɗaya daga cikin Ƴan Dabar da suka kashe kwamandan Bijilante a Ja’en Ƴan Dillalai – Ƴan Sanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke mutum daya daga cikin ƴan dabar da ake zargin sun kashe kwamandan ƙungiyar Bijilante na unguwar Ja’en Ƴan Dillalai a jihar Kano, mai suna Muhktar Garba, wanda akafi sani da Baballiya.

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatarwa gidan rediyon Dala FM Kano, kama matashin, Kiyawa ya ce bayan samun rahoton faruwar faɗan dabar a tsakanin ƴan unguwar Ja’en Maƙera, da kuma wasu ƴan unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, ne aka tura jami’an ƴan sanda da suka samar da tsaro a yankin.

“Daga rahotannin da muká samu faɗa ne na ƴan Daba, da ya kaure a tsakanin ƴan unguwar guda biyu a daren ranar Talata, inda ƴan dabar suka rufe kwamandan Bijilanten da sara da makamai har ta kai ga sun yi masa illa bayan an kai shi Asibiti ya rasu, “in ji Kiyawa”.

Ya kuma ce zuwa yanzu akwai wani mutum ɗaya daga cikin ƴan dabar da aka gane shi kuma yana hannun ƴan sanda a babban sashin binciken manyan laifuka ɓangaren kisan kai ana faɗaɗa bincike.

SP Kiyawa, ya ƙara da cewa rahotannin da suka samu daga jami’an su yanzu haka komai ya fara dai-dai ta ƙura ta lafa, inda mutane suke gudanar da al’amuran su na yau da kullum.

A daren jiya ne dai aka zargi wasu ƴan Daba daga unguwar Ja’en Maƙera, sun shiga unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, inda suka haifar da faɗan Daban, lamarin da har suka kashe kwamandan Bijilanten na Ƴan Dillalai, wanda tuni akayi jana’izar sa a safiyar Larabar nan.

Continue Reading

Trending