Connect with us

Hangen Dala

Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar EFCC

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Ola Olukoyede a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) na tsawon shekaru hudu a matakin farko, har sai Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi.

 

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce Olukoyede lauya ne wanda ke da gogewa sama da shekaru 22 kuma kwararre ne.

 

“Yana da gogewa sosai a harkokin hukumar EFCC, inda a baya ya rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa (2016-2018) da kuma sakataren hukumar (2018-2023). Don haka, ya cika sharudan da doka ta gindaya na nada shi a matsayin Shugaban Hukumar EFCC.

 

“Nadin Olukoyede ya biyo bayan dakatar da Mista Abdulrasheed Bawa,” in ji shi.

 

Bugu da kari, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce shugaba Tinubu ya amince da nadin Muhammad Hassan Hammajoda a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa na tsawon shekaru biyar a matakin farko, har sai majalisar dattawa ta tabbatar da shi.

 

“Muhammad Hassan Hammajoda ma’aikacin gwamnati ne wanda ya kware a harkar hada-hadar kudi na gwamnati wanda ya yi digirin digirgir a fannin lissafi a jami’ar Maiduguri da kuma digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci.

 

“Ya fara aiki a matsayin malami a Federal Polytechnic, Mubi. Daga nan ne ya shiga aikin banki, ciki har da wanda ya yi nasara a bankin Allied da Standard Trust Bank.

 

“Shugaba Bola Tinubu ya dorawa sabon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta’annati (EFCC) aiki domin tabbatar da amincewar da aka basu a wannan muhimmin aiki na kasa a matsayin sabon yaki da cin hanci da rashawa da ake yi ta hanyar sake fasalin hukumomi a bangaren yaki da cin hanci da rashawa,” in ji shi.

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Baba Suda

Dumamar yanayi :- Gwamna Zulum ya haramta sare bishiyu

Published

on

Gwamnan jihar Borno Baba Gana Umar Zulum ya kaddamar da wasu dokokin biyu ga al’ummar Jihar.

Dokar farko itace Gwamnan ya haramta sare bishiyu a dukkanin fadin jihar, Inda kuma ya Kara kaddamar da dokar tsaftace muhalli a dukkanin karshen wata.

 

Yayin da yake kaddamar da dokar Gwamna Zulum yace duba da dumamar yanayi da ake fuskanta a yanzu gwamnati ta haramta sare bishiyu a fadin jihar Borno.

Haka kuma saboda Kare lafiya da kuma al’ummar Jihar dole ne dukkanin karshen wata a gudanar da tsaftar muhalli a Jihar Borno.

 

” A matsayi na Wanda kundin tsarin mulkin kasa ya bani dama, ni Baba Gana Umara Zulum na haramta sare bishiyu a fadin jihar Borno, kuma na saka dokar wajibi ne kowa ne dan Jihar ya tsaftace muhalli a dukkanin karshen wata, saboda inganta lafiyar al’ummar Jihar Borno.”

Continue Reading

Trending