Connect with us

Labarai

Muhyi ya kama Wanda ake zargi da sayar da filayen gwamnati

Published

on

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano (PCACC) , ta cafke wani mutum mai suna Musa Salihu Ahmed, bisa zarginsa da almundahanar da biliyan 2.3, inda yake amfanin da sunan kamfanin Lamash ana cinikin filayen.

Shugaban hukumar na jahar Kano Barista Muhuyi Magaji Rimingado ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Muhuyi Rimingado, ya ce wanda ake zargin, an cafke shi a filin jirgin saman na Mallam Aminu Kano, bayan ya dawo daga kasar Saudiya, bisa zargin siyar da filayen gwamnatin kan naira miliyan biyu da dubu dari biyar kowannensu.

Hukumar ta kara da cewa, filayen suna unguwar Chalawa a karamar hukumar Kumbotso da kuma Dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

Rimingado ya ce sun fara gudanar da bincike kan zargin yadda gwamnatin da ta gabata, ta ware masa wasu filaye 632, inda yake sayarwa da daidaikun jama’a.
Kuma da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da Wanda ake zargi a gaban kotu.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending