Connect with us

Labarai

Ba zamu saurarawa ‘yan dabar da suka addabi mutane ba – ‘Yan Sandan Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta lashi takobin kakkabe bata garin da suke kara addabar al’umma a sassan jihar Kano.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan ga manema labarai, biyo bayan yadda ake samun karuwar ta’addanci a sassan Kano.

Ya ce sun samu rahoton guda daga cikin tubabben dan adabar nan da ya balle ya koma ruwa, mai suna Bahago Affa Kuka Bulukiya, yake hada gungun ‘yan Daba suna addabar mutane a yankin Dala da kewayenta da kuma yankin Gwale da kewayensu a jihar ta Kano.

“Kasancewar ta’addancin yana haifar da fargaba a wannan jaha ta Kano dan haka ya zama wajibi mu magance matsalar tsaron; Zamu kama tare da mika ‘yan dabar gaba domin daukar mataki akansu, “in ji CP Gumel”.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

Ya kuma ce yanzu haka jami’ansu sun baza koma domin kamo ‘yan dabar da suka addabi mutane da suka hada da Walidi Lungun ‘yan Kifi, Kabiru KB Show, da Wando Filin Kutare, sai kuma Tele Durumin Daje, Mamman Kan Tudu, da dai sauran sunayen wasu mutane da suke a cikin wata takarda da rundunar ‘yan sandan ta rubutu, da take nema ruwa a jallo.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending