Connect with us

Labarai

‘Yan fashi sun kaddamar da hare-hare a wasu unguwanni da ke birnin Kano

Published

on

Da daren ranar Talata ne wasu ‘yan fashi da makami suka kaddamarwa wasu yankuna a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Maharan dauke da makamai a cikin wata mota sun farwa wurare da dama a inda ake hada-hadar kasuwanci, tare da harbin kan mai uwa dawabi.

Ko da yake kamar yadda rahotanni suka tabbatar, ba a samu asarar rayuka ba, sai dai sun kwace kudade a hannun masu shaguna.

Mutane da dama ne suka nemi tsira da ransu, yayinda maharan suka fara harbin kan mai uwa dawabi.

da farko dai maharan sun kai hari rukunin shagunan Shy Plaza da ke unguwar kofar Gadon Ƙaya a birnin Kano.

Lamarin ya faru ne bayan ƙarfe bakwai na daren ranar Talata.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa Dala FM cewa, ƴan fashin sun zo ne su huɗu a mota ɗauke da bindigu inda suka riƙa harbin iska a sama.

“Su na zuwa sai suka fara harbe-harbe suna ce mana ku shiga ciki, to dama mai wannan shagon da yake kusa da ni ya riga ya shiga ciki, sai suka bi shi.” In ji shi

Daga nan ne kuma mutane suka shiga gudu, su kuma suka shiga wasu shaguna biyu na sayar da kwamfiyuta da kuma shagon hada-hadar kuɗi na POS suka yi awon gaba da kayayyaki.

Ɗaya daga cikin masu shagunan da lamarin ya shafa Musaddiƙ Sidi Bala ya shaida wa Dala FM cewa, ƴan fashin sun yi awon gaba da kwamfiyutoci na sama da naira miliyan ɗaya, baya ga wayoyin hannu.

To haka abun ya kasance a Unguwar Tukuntawa, inda suka kwashe kudin wani shago sama da 400,000.

Har kawo yanzu hukumomin tsaro a Kano ba su ce komai ba kan faruwar lamarin.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending