Connect with us

Manyan Labarai

Kamfanin BUA ya ce zai ci gaba da sayar da sumuntinsa kan 3,500

Published

on

Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Isyaka Rabi’u, ya ce kamfaninsa zai cika alkawarinsa na ci gaba da sayar da sumunti kan farashin 3,500 daga watan Janairun shekarar 2024 mai kamawa.

Abdussamad ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawarsa da manema labarai, bayan ziyara da ya kai wa shugaban kasa Bola Ahmas Tinubu a gidansa da ke jihar Legas ranar Alhamis din nan.

“Kamfanina zai kuma tabbatar da cewa sumuntin ya wadata da kuma sauki ga kwastomomin mu duk da kalubale da ake ciki a yanzu, ‘in ji Abdussamad”.

Ya kuma ce sun saka farashin sumuntin kan Naira 3,500 a kan kowane buhu, inda za kuma su duba kuɗin haraji da kuma nisan yankin da za a kai sumunti.

Ya ci gaba da fadawa Tinuhu, “Kamar yadda ka sani, muna da kamfanoni guda biyu; ɗaya a Edo, yayin da ɗaya muke yake jihar Sokoto. Alal misali, idan kana son mu kai maka sumunti daga Sokoto zuwa Legas ko Adamawa ko kuma Maiduguri, idan ka duba yana da nisan gaske,” in ji BUA.

Ya kara da cewa duk da cewa idan aka yi la’akari da nisa ko kuma wurin da za a kai sumunti farashin zai iya tashi, amma kamfanin zai cika alkawarinsa inda zai ci gaba da sayarwa a kan 3,500, duk buhu daya.

“Za kuma a kaddamar da kamfanin sumunti da ke Sokoto a watan Janairun 2024, wanda hakan zai sa mu faɗaɗa kasuwancin mu a faɗin ƙasar nan, “A cewarsa”.

Daga bisani dai Abdussamad Rabi’u ya ce ya kai wa shugaban ƙasar ziyara ne domin yi masa gaisuwar Kirsimeti da kuma ta sabuwar shekara mai kamawa.

Manyan Labarai

Uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a Kano sun rasu

Published

on

Rahotanni da dumi-ɗumin sa na bayyana cewar yanzu haka uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a unguwar Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano sun rasu.

Wani mazaunin garin ya shaidawa Dala FM Kano, da tsakar ranar Larabar nan cewar, daga cikin mutane ukun da suka rasu har da limamin da ya jagorancin sallar asubar wannan rana, wanda a lokacin ne matashin ya cinna musu wutar lamarin da jikin su mutanen sama da 20 ya sassaɓule.

Idan dai ba’a manta ba matashin ya cinnawa mutanen wuta ne bayan da ya watsa Fetur cikin masallacin yayin da suke tsaka da sallar Asubah, ta wannan rana, wanda tuni jami’an tsaron ƴan sanda suka cika hannun su da shi.

Matashin dai ya ce ya cinnawa mutanen wutar ne biyo bayan wata magana da suke faɗa masa wanda ransa baya daɗi, ina ya sayo Fetur a cikin wani Galan lamarin da yaje ya kunna musu wutar, duk da shima hannayen sa biyu sun ƙone.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun kama matashin da ya kunnawa mutane sama da 20 Wuta a cikin wani masallaci – Ƴan Sandan Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da cinnawa wasu mutane Wuta, a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubar yau Laraba, a cikin wani Masallaci a garin Larabawar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano, a yau Laraba, ya ce bayan samun rahoton faruwar al’amarin ne Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya tura tawagar jami’an su inda suka kai ɗaukin gaggawa.

Matashin da ake zargin mai suna Shari’u Abubakar ɗan shekaru shekaru 38, ya ce shine ya siyo Fetur ya kunna wutar inda ya wurgata a cikin masallacin, lamarin da ya sa mutane da dama suka ƙone a sassan jikin su.

“Aƙalla mutane 24 ne suka ƙone bayan da matashin ya kunna musu wutar a cikin masallacin, wanda tuni jami’an mu suka kai su asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci, “in ji SP Kiyawa”.

Koyawa, ya kuma ce daga binciken farko da suka fara matashin ya tabbatar da cewa shine ya sayo Mai a gidan Mai a cikin wata roba, yazo ya kunna wutar, biyo bayan wani rikicin gado da a tsakanin sa da wasu daga cikin mutanen yankin su, inda shima hannayen sa biyu suka ƙone.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sama da mutane 20 ne suka ƙone a sassan jikin su bayan da ake zargin wani abu ya fashe a cikin wani masallaci da ke Kano

Published

on

Rahotanni na nuni da cewa an yi zargin fashewar wani abu da asubahin wannan rana ta Laraba, a garin larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar kano, wanda kuma ya jikkata sama da mutane 20, sakamakon ƙonuwa a sassan jikinsu.

Yanzyu haka dai da yawa daga cikinsu sun fara karɓar agajin
gaggwa a babban asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, da ke Kano, kamar yadda wani ganau ya shaidawa
gidan rediyon Dala FM, lokacin da ya ziyarci asibitin a safiyar wannan
rana.

Sai dai wani da ya tsallake rijiya da baya mai suna Yusuf Abdullahi, ya ce yana cikin masallacin lokacin da lamarin ya faru suna tsaka da Sallah Asuba aka kunna wutar daga waje inda aka cillota cikin masallacin, saɓanin abin fashewar da wasu suke faɗa.

Ya kuma ce, “Allah ne kawai ya bani ikon fita Amma mutane da yawa ciki har da yan uwana guda biyu lamarin ya rutsa da su, kuma wutar ta yi musu illa babba saboda ko kasan mutum wallahi idan ka gan shi wallahi ba za ka iya gane shi ba”. Inji Yusuf Abdullahi”.

Wakilin Dala FM, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki, ya tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar tarho, sai dai ya ce yanzu haka
yana kan aikin tattara bayanai akan al’amarin, wanda rundunar
za ta fitar nan gaba kaɗan.

Continue Reading

Trending