Connect with us

Manta Sabo

An ci gaba da shari’ar neman rami tsakanin Alh. Aminu Dantata da iyalan Sharu Ilu a Kano

Published

on

Kotun daukaka kara dake nan zamanta a sakatariyar Audu Bako a nan Kano, ta ci gaba da sauraron shari’ar nan da ake yi tsakanin iyalan marigayi Sharu Ilu da Alhaji Aminu Alhassan Dantata da wasu mutane hudu.

Tunda fari dai Alhaji Aminu Alhassan Dantata ne ya daukaka karar a kotun, akan wani rami dake unguwar Gwammaja, da iyalan marigayi Sharu Ilun suka ce nasu ne, bayan da babbar kotun jaha ta yi hukunci inda ta mallakawa iyalan Sharu Ilun.

A zaman dai na yau, kotun daukaka karar ta kammala sauraron lauyoyin kowanne bangare inda ta dage zaman domin yin nazari akan shari’ar tare da sanya ranar yanke hukunci.

Bayan fitowa daga kotun ne muka so jin ta bakin lauyar mai kara Barista Beronika Anita, sai dai hakar mu bata cimma ruwa ba, a nan ne muka wai-wayi lauyan wadanda akayi karar Barista Ma’arfu Kasim, wanda ya yiwa wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u karin bayani akan shari’ar, inda ya ce suna fatan yi musu adalci a shari’ar.

Kafun dai daukaka karar akalla an shafe shekaru sama da hudu ana shari’ar akan batun ramin.

Manta Sabo

Wata Kotu a Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar da aka shigar da ƙaramar hukumar Gwale da wani mutum

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 15 da ke zamanta a Mila Road a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta ci gaba da saurarar karar da al’ummar unguwar Dorayi Baba unguwar jakada suka shigar da karamar hukumar Gwale, da wani mutun mai suna Alhaji Ibrahim Ƴan Shana.

Tunda fari dai mutanan unguwar sun shigar da karar ne suna zargin karamar hukumar ta Gwale, da cefanar wa Ibrahim ‘yan Shana wani fili mallakin al’ummar unguwar na makaranta, lamarin da su garzaya gaban kotun tun a shekarar 2023, a lokacin shugabancin ƙaramar hukumar da ya shuɗe, suna rokon da ta dawo musu da shi domin a gida makaranta a yankin nasu.

Sai dai a zaman kotun na yau bangaren wadanda ake kara na daya wato karamar hukumar Gwale sun gaza gabatar da martanin su akan karar, inda suka roki kotun da ta sanya wata ranar domin gabatar da martanin nasu.

Wakilimmu Mu’az Musa Ibrahim ya rawaito cewa mai shari’ar ya sanya ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2024 domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta aike da matashin da ake zargi da kashe matar sa gidan yari a Kano

Published

on

Kotun majistret mai lamba 29 karkashin jagorancin mai Shari’a Talatu Makama, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.

Matashin mai suna Adamu Ibrahim ana zargin sa ne da laifin hallaka mai ɗakinsa ta hanyar kwantara mata dutsen Guga, a fuskarta a can garin kwanar ɗan gora.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar, tun a ranar 9 ga watan 4, wani mai suna Idris Adamu yaje caji ofishin ƴan sanda inda ya shigar da kara akan cewar Adamu Ibrahim ya kashe mai ɗakinsa wadda kuma kanwa ce a wajen mai ƙarar Idris Adamu.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’ila, ya zanta wanda ake zargi wanda ya ce tsautsayinya sanya shi aikata hakan.

Shima dan uwan marigayiyar ya bayyana matsayarsu, inda ya roƙi kotun da ta yi musu adalci a shari’ar.

Kotun dai ta sanya ranar 17 ga watan gobe dan a kara gabatar da shi a gaban ta domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Trending