Connect with us

Manta Sabo

Kalaman Tunziri: Kotu ta aike da Dan Bilki Kwamanda dake Kano gidan yari

Published

on

Yanzu haka wata kotu a jihar Kano ta aike da Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda dan jam’iyyar APC a jihar Kano, gidan yari bisa zargin yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma a cikin al’ummar jihar.

Tun da farko dai rundunar tsaron farin kaya ta DSS ce ta gayyaci Danbilki Kwamanda din wanda tsohon makusanci ne ga tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kafin daga bisani su gurfanar da shi gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bata suna da tunzura al’umma.

Yanzu haka dai Dan Bilki zai ci gaba da zama a gidan yari har zuwa ranae 29 ga watan Janairun shekarar 2024.

Sai dai jim kaɗan da tura shi gidan gyaran halin Danbilki Kwamanda ya bayyana cewa gwamnatin Kano ce ta gurfanar da shi ba hukumar DSS ba a shafinsa na Facebook a yau.

“Ba DSS ne suka kaini kotu ba gwamnatin Jihar Kano ce ta kaini kotu, kuma duk abinda aka yi shiryawa a ka yi. DSS sun gayyaceni kuma na amsa gayyata ni ne na kai kaina wurisu sun kuma yi abinda shi ne doka. Abinda muke son alƙalai su rinka yi su de na aiki da umarnin wani su yi aiki da doka domin Allah zai tambayesu kowanne hukunci da su ka yi” In ji shi”.

Ana tuhumarsa da ɓatawa tsohon gwamnan Kano Senata Rabi’u Musa Kwankwaso suna, kan zargin cewar ya umarci gwamnatin Abba Kabir Yusuf na yunƙurin rushe masarautun da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirkiro tare kuma da yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Manta Sabo

Wata Kotu a Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar da aka shigar da ƙaramar hukumar Gwale da wani mutum

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 15 da ke zamanta a Mila Road a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta ci gaba da saurarar karar da al’ummar unguwar Dorayi Baba unguwar jakada suka shigar da karamar hukumar Gwale, da wani mutun mai suna Alhaji Ibrahim Ƴan Shana.

Tunda fari dai mutanan unguwar sun shigar da karar ne suna zargin karamar hukumar ta Gwale, da cefanar wa Ibrahim ‘yan Shana wani fili mallakin al’ummar unguwar na makaranta, lamarin da su garzaya gaban kotun tun a shekarar 2023, a lokacin shugabancin ƙaramar hukumar da ya shuɗe, suna rokon da ta dawo musu da shi domin a gida makaranta a yankin nasu.

Sai dai a zaman kotun na yau bangaren wadanda ake kara na daya wato karamar hukumar Gwale sun gaza gabatar da martanin su akan karar, inda suka roki kotun da ta sanya wata ranar domin gabatar da martanin nasu.

Wakilimmu Mu’az Musa Ibrahim ya rawaito cewa mai shari’ar ya sanya ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2024 domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta aike da matashin da ake zargi da kashe matar sa gidan yari a Kano

Published

on

Kotun majistret mai lamba 29 karkashin jagorancin mai Shari’a Talatu Makama, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.

Matashin mai suna Adamu Ibrahim ana zargin sa ne da laifin hallaka mai ɗakinsa ta hanyar kwantara mata dutsen Guga, a fuskarta a can garin kwanar ɗan gora.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar, tun a ranar 9 ga watan 4, wani mai suna Idris Adamu yaje caji ofishin ƴan sanda inda ya shigar da kara akan cewar Adamu Ibrahim ya kashe mai ɗakinsa wadda kuma kanwa ce a wajen mai ƙarar Idris Adamu.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’ila, ya zanta wanda ake zargi wanda ya ce tsautsayinya sanya shi aikata hakan.

Shima dan uwan marigayiyar ya bayyana matsayarsu, inda ya roƙi kotun da ta yi musu adalci a shari’ar.

Kotun dai ta sanya ranar 17 ga watan gobe dan a kara gabatar da shi a gaban ta domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Trending