Connect with us

Manyan Labarai

Matsalar Tsaro: Majalisar dattawa ta yi sammacin manyan hafsoshin sojin Najeriya

Published

on

Yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a sassan jahohin Najeriya, majalisar dattawan kasar ta yi sammacin manyan hafsoshin tsaron kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan majalisar sun bukaci hakan ne a karkashin murya guda bayan wani zaman gaggawa da suka yi bayan dawowarsu bakin aiki karon farko a wannan shekarar ta 2024.

Hakazalika majalisar dattawan ta yi zaman gaggawar ne bayan da shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da kuduri amadadin sanatocin kan yanayin tsaron da ake fuskanta a kasar.

Majiyar BBC ta rawaito bayan shafe kusan sa’a biyu ‘yan majalisar suna taron sirri, sun sake haduwa tare da yanke shawarar gayyato manyan hafsoshin tsaro a mako mai zuwa game da karuwar rashin tsaron a Najeriya.

Dukkanin manyan hafsoshin tsaron sun hadar da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, da shugaban rundunar sojin kasa, Leftenant Taoreed Lagbaja, da shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, sai kuma shugaban rundunar sojin ruwa Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Daga bisani ne dai majalisar ta kuma dage zamanta zuwa 6 ga watan gobe na Fabarairu, domin bai wa ‘yan majalisar damar yin zabe a zaben cike gurbi na ranar Asabar mai zuwa.

A baya-bayan nan, an ga karuwar matsalar tsaro a Abuja, babban birnin kasar da jihar Filato da kuma wasu sassan Najeriya, da aka samu karuwar garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da kashe-kashe, wanda na baya-bayan nan shi ne kisan wasu sarakunan gargajiya da kuma sace daliban makaranta da malamai a jihar Ekiti.

Idan ba’a manta ba ko a ranar Talata 30 ga watan Janairun 2024, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya soki Shugaba Bola Tinubu da yin tafiye-tafiye yayin da kasar ke fama da matsalolin tsaro sai dai a martaninta, gwamnati ta ce tana yin duk mai yiwuwa domin dakile matsalar tsaron.

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending