Connect with us

Labarai

Tinubu ya mika ta’aziyyar tsohon gwamnan Yobe Alhaji Bukar Abba

Published

on

Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar, tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim, wanda ya rasu jiya Lahadi a kasar Saudiyya.

Wannan na cikin sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Lahadi, Tinubu ya ce al’umma za su tuna shi a matsayin jajirtaccen shugaba da ya yi hidima wajen gina rayuwar mutane da kasa baki daya.

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayin da rahama Amen.

Tsohon gwamnan ya rasu ne, a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sakataren Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mamman Mohammed, ya tabbatar da rasuwar.

Mamman ya ce za a yi jana’izar marigayin a Saudiyya, inda kuma za kuma a yi zaman makokin rasuwar sa a Jihar Yobe, mahaifar sa.

Labarai

Ƴan Majalisu, Malamai, da gwamnoni ya kamata ku faɗawa Tinubu gaskiya kan halin da Talakawa suke ciki – Human Right 

Published

on

Ƙungiyar kare hakƙin ɗan adam ta Sustainable Growth Initiatives for Human Right Development, ta ce akwai buƙatar Sanatoci, da ƴan majalisar tarayya da kuma Malamai, su faɗawa shugaban ƙasa Bola Tinubu gaskiya wajen yin abinda ya dace kan tsadar rayuwar da al’umma suke ciki, biyo bayan janye tallafin man fetur, da kuma ƙarin farashin da suke samu.

Daraktan ƙungiyar a matakin ƙasa Kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ne ya bayyanawa Dala FM hakan, a wani ɓangare na nuna takaicin sa kan yadda daga lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗare karagar mulki kukan al’umma ya ƙara ninkuwa, al’amarin da ke damun su.

Kwamared Abubakar Musa ya ce yadda al’ummar ƙasa suke ci gaba da fuskantar halin tsadar rayuwa, kamata ya yi ta fito da sabbin tsare-tsaren da za su taimake su, ba wai yin abinda zai ci gaba da musguna musu ba.

A cewar sa, “Daga lokacin da kuɗin man fetur ya nunka to komai ma ninkawa yake yi wanda harkokin kasuwanci, da cin Abinci ga mutane, da sauran buƙatu duk suka ɗai-ɗai ce, a don haka ya kamata Sanatoci, da Ƴan Majalisar Wakilai, da gwamnoni, da dukkanin masu ruwa da tsaki ku yi abinda ya dace domin ganin al’umma sun samu sauƙi, “in ji shi”.

Kwamared Abubakar ya ƙara da cewar ya kamata suma malamai su tashi tsaye wajen faɗawa shugabanni gaskiya, wajen ganin sun tausayawa al’umma domin samun mafita daga acikin yanayin tsadar rayuwar da suke ciki a ƙasa.

Al’ummar ƙasar nan dai sun sake shiga cikin mawuyacin hali ne tun bayan da shugaba ƙasa Bola Tinubu ya ayyana janye tallafin man fetur, jim kaɗan da rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Yanzu haka dai mafi yawan gidajen man ƴan kasuwa a sassan jihar Kano, suna sayar da kowacce litar Fetur ɗaya akan kuɗi Naira 11,00, wasu kuma 1150, zuwa 1,200, yayin da na NNPCL ke sayar da kowacce lita ɗaya 10,30, a Arewa maso Yammacin Najeriya, abin da ke damun al’umma, ki da dai a wasu ɓangarorin ƙasar yake zarta hakan.

Continue Reading

Labarai

Ya kamata gwamnan Kano ya yi koyi da gwamnonin da suka fara biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi – Human Right

Published

on

Ƙungiyar wayar da kan jama’a da kare haƙƙin ɗan adam da tallafawa mabuƙata, ta Awareness for Human Right and Charity Foundation, ta yi kira ga gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya yi koyi da gwamnatin jihar Adamawa da Kogi, wajen biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, bisa halin matsin rayuwar da ake ciki.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Auwal Usman Awareness, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM a ranar Talata, ya ce duba da halin matsin rayuwar da ake ciki, akwai buƙatar gwamnanan ya ƙara wai-waye ga kwamitin da ya kafa akan duba fara biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashin na Naira dubu 70,000.

Kusan dai watanni biyu ke nan da gwamnatin jihar Adamawa ta fara biyan ma’aikatan ta mafi ƙarancin albashin, wanda a ranar Litinin shima gwamnan jihar Kogi Usman Ododo, ya sanya hannu kan ƙarancin albashi da za’a fara biyan ma’aikatan Naira 72,000 daga wannan wata na October.

Kwamared Auwal Awareness ya ƙara da cewa fara baiwa ma’aikatan jihar nan mafi ƙarancin albashin ka iya taimaka musu wajen rage musu wani raɗaɗin tsadar rayuwar da ake ciki a yanzu.

Tuni dai hankalin ma’aikata da dama ya karkata kan ganin cewar an fara biyan su mafi ƙarancin albashin a jihar nan da ma jahohin da ba’a fara ba, domin ƙara samun dama wajen magance wasu daga cikin matsalolin su na yau da kullum.

Continue Reading

Labarai

Ku kasance masu neman Ilmi domin sanin kan ku – Human Right

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta buƙaci al’umma da su tashi tsaye wajen neman Ilmi ta yadda za su san kan su, tare da sanin hanyoyin da ake bi wajen neman haƙƙi yayin da aka danne musu.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai, a wani ɓangare na taron ƙarawa juna sani akan aikace-aikacen ƙungiyar da ma abinda ya shafi hulɗa da jami’an tsaro, da ƙungiyar ta gudanar ranar Lahadi a Kano.

Kwamared Tasi’u Idris ya kuma ce a shirye ƙungiyar tare wajen ƙara kyautata alaƙar ta da jami’an tsaro, domin ganin an ci gaba da gudanar da ayyukan al’umma cikin nasara ba tare da fuskantar matsala ba.

Da yake nasa jawabin masanin tsaron nan Ditective Auwal Bala Durumin Iya, shawartar ƴan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ya yi, da su ƙara himma wajen neman ilmin aikin da suke yi, wanda hakan ka iya taimaka musu wajen kaucewa fuskantar matsala.

Shima a nasa ɓangaren Dagacin garin Sharaɗa Alhaji Ilyasu Mu’azu Sharaɗa, kira ya yi ga ƴan ƙungiyar da su ƙara da kiyaye dukkanin abinda ka iya haifar musu da matsala yayin gudanar da ayyukan su.

Majiyar Dala FM Kano ta rawaito cewa yayin taron al’umma da dama ne suka samu damar halarta, kuma ciki har da Kakakin rundunar tsaro ta Civil Defense SC Ibrahim Idris Abdullahi, wanda ya samu Wakilcin mataimakin sa AS Abdulmajeed, da ƴan ƙungiyar

Continue Reading

Trending