Connect with us

Manta Sabo

Kotu ta yi umarnin a duba kwakwalwar Cucu da ake zargi da kashe abokin kasuwancin ta

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 13 karkashin jagorancin mai shari,a Zuwaira Yusuf, ta fara sauraron karar da gwamnatin kano ta shigar tana karar wata mata mai suna Hafsat Surajo da wasu mutane uku.

Gwamnatin jaha dai tana zargin Hafsat da laifin kashe wani matashi ta hanyar caka masa wuka a kirji da ciki, a ranar 21 ga wata 12 na shekarar da ta gabata ta 2023.

Ana kuma zargin wasu mutane da laifin hada baki da boye gaskiya da yunkurin kawar da shaida akan laifin kisan kai.

Mutanen da ake zargin sun hadar da mijin Hafsat wato Dayyabu Abdullahi, da Adamu Muhammad da kuma Nasidi Muhammad, dukkaninsu sun musanta zarge-zargen da ake musu.

Ita kuwa Hafsa da ake zargi da laifin kisan kai taki cewa komai a gaban kotun.

A yayin zaman lauyar gwamnati Barrister Aisha Mahamud, ta roki kotun cewar a yi umarni likitici su binciki lafiyar Hafsat, kotun ta amince da rokon.

Lauyoyin wadanda ake kara sun roki kotun ta sanya su a hannun beli sai dai lauyoyin gwamnati sun yi suka.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa kotun ta ce za ta sanya rana dan bayyana ra’ayinta.

Manta Sabo

Wasu ƴan mata sun tayar da bori a kotu bayan an tsalala musu Bulala

Published

on

Kotun majistret mai lamba 51 ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Hajara Safiyo Hamza, ta hori wasu ƴan mata da ɗaurin watanni 6, ko kuma zabin tarar dubu tamanin-tamanin kowanne su, da kuma karin bulala shida-shida haɗi da sharar banɗaki ta sati uku.

Tunda fari Ƴan Sanda ne suka gurfanar da ƴan matan bisa zargin su da yawan banza, da tayar da hankalin al’umma, da kuma laifin Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Yayin da aka karantawa ƴan matan ƙunshin tuhumar da ake yi musu sun amsa laifin nasu har guda goma sha Shida.

A yayin zaman kotun ta tambaye su dalilin da ya sanya suke yawon banza, inda suka bayyana mata cewar suna fitowa ne daga gaban iyayensu idan sun kammala yawace-yawacen sai su koma gida.

Mai Shari’a Hajara Safiyo ta kuma umarci ƴan matan da su zama mutanen kirki idan sun gama zaman gidan gyaran halin.

Wakilin Dala FM Kano Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar, jim kaɗan bayan kammala hukuncin sai ƴan matan suka fara koke-koke hadda hawa bori a kotun, bisa shiga furgicin da suka yi kan hukuncin.

Continue Reading

Manta Sabo

Zargin Karuwanci: Kotu ta aike da wasu ƴan Mata su 17 gidan gyaran hali

Published

on

Kotun Majistret mai lamba 51 ƙarƙashin mai Shari’a Hajara Safiyo Hamza, da ke jihar Kano, ta aike da wasu ƴan mata gidan ajiya da gyaran hali.

Tunda fari ƴan matan aƙalla su kimanin 17 an kama su ne a unguwar Sabon gari da ke jihar Kano, suna yawon ta zubar da kuma karuwanci.

Ƴan matan waɗanda aka gabatar da su a gaban kotun a wani yanayi na rashin kyan gani, sun bayyanawa kotun shekarunsu waɗanda suka kama daga shekara 18, zuwa 19, an kuma karanta musu zarge zargen da ake yi musu na yawan banza da karuwanci da kuma tayar da hankalin al’umma da shaye-shaye, inda suka amsa nan take.

Mai gabatar da ƙara Haziel, ya roƙi kotun da ta sanya wata rana dan a yi musu hukunci, domin iyayensu su bayyana a gaban kotun.

Kotun ta aike dasu gidan gyaran hali zuwa ranar 16 ga watan nan dan iyayensu su bayyana a gaban kotu, inda nan da nan suka ruɗe da Kuka

Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar, yayin zaman wasu samari sun cika kotun da zummar su biya musu tara, sai dai kasancewar ba’a sanya su a hannun belin ba, a nan ne jami’in gidan gyaran hali Nasiru Dogarai ya tisa ƙeyarsu zuwa gidan gyaran hali.

Continue Reading

Manta Sabo

Wata mata ta tayar da hayaniya ana tsaka da shari’a a kotu

Published

on

Kotun majistret mai lamba 51 karkashin mai Shari’a Hajara safiyo Usman, ta aike da wata mata asibitin kwakwalwa na Dawanau dan a binciki lafiyar ƙwaƙwalwar ta.

Tunda farko wani mutum ne mai sauna Ibrahim Muhammad, ya shigar da ƙara bisa yadda ya yi zargin cewar, matar ta doke shi da wani ƙarfe dan kawai ya tashe ta daga gidan da take haya.

Mai ƙarar ya bayyana cewar, kotu mai lamba 23 ta tashi matar daga gidan amma sai ta ɓalle ƙofar gidan ta sake dawowa gidan, ko da yaje dan jin dalili sai ta bubbuga masa wani ƙarfe.

Yayin da ake karanta mata ƙunshin tuhumar matar ta tayar da hayaniya a gaban kotun, har ma ta bayyanawa mai Shari’a cewar, duk wanda ya koma gidanta da niyar fitar mata da kaya kwanansa ya ƙare.

Daga nan ne mai Shari’a Haraja Safiyo, tayi umarnin da akai matar asibitin Ƙwaƙwalwa na Dawanau da ke jihar Kano, domin a duba lafiyar ta, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito.

Continue Reading

Trending