Connect with us

Labarai

Likitoci ku fi mayar da hankalin yin aiki a Gida mai-makon fita ƙasashen waje – Dr. Binta Jibril

Published

on

Shugabar Asibitin yara na Khalifa Isyaka Rabi’u da ke jihar Kano, Dakta Binta Jibril Wudil, ta ce akwai buƙatar likitoci masu tasowa su fi mayar da hankalin yin aiki a Gida mai-makon fita ƙasashen waje bisa irin ƙalubalen da matan ke fuskanta.

Dakta Binta Jibril Wudil ta bayyana hakan ne yayin zantawar ta gidan rediyon Dala FM Kano, a wajen taron wayar da kan likitoci mata masu tasowa da ƙungiyar Likitoci Mata ta ƙasa reshen jihar Kano ta Medical Women’s Association (MWAN) ta gudanar ranar Asabar a ɗakin taro na Asibitin Yara na Khalifa Isyaka Rabi’u.

“Ba za ace babu alfanu da ake samu ba yayin aikin a ƙasashen ƙetaren amma ƙalubalen da likitocin suke fuskanta musamman ma Mata a ƙasar wajen yafi yawa, a dan haka ta shawarce su da su rinƙa aikin su a gida yafi, domin “kowa yabar Gida, Gida ya barshi”, in ji Dr. Binta”.

Da take nata jawabin shugabar ƙungiyar likitoci Mata ta ƙasa reshen jihar Kano, Dakta Halima Adamu, ta ce sun shirya taron ne domin baiwa likitoci masu tasowa shawarwari akan aikin ta yadda za su cimma nasara ba tare da sun samu wata matsala ba.

Dakta Halima ta kuma ce daga cikin shawarwarin akwai irin ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasashen waje da kuma alfanu, inda tace akwai buƙatar idan ma za su fita ƙasar wajen su rinƙa fara taimakon al’ummar ƙasar su tare da mayar da hankalin aiki a Gida.

A nata ɓangaren ƙwararriyar likitar mata masu juna biyu da sanin matsalolinsu, a asibitin Mallam Aminu Kano, kuma Malama a jami’ar Bayero dake jihar Kano, Dakta Zainab Datti Ahmad, ta ce aƙalla ta shafe shekaru biyu tana aiki a ƙasar Saudiyya, amma a yanzu yin aiki a Gida yafi mata, a dan haka ne ma ta shawarci likitoci masu tasowa idan suna da sha’awar fita wajen da su fara gina kansu a Gida.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa a yayin taron manyan likitoci mata da dama ne suka bayar da maƙala ga likitoci masu tasowa, ta yadda zasu gudanar da ayyukasu cikin nasara.

Labarai

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ya tsallake karatu na ɗaya a majalisar dokokin Kano

Published

on

Ƙudurin gyaran dokar gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren majalisar dokokin jihar.

Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan da akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Ɗiso, ya gabatar da karatun na ɗaya.

Har ila yau, yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta tallafa wa wasu kanikawa da kafintoci bisa iftila’in gobarar da ta ƙone musu kaya na miliyoyin Naira, tare da asarar rayuka a kan titin Lawan Dambazau.

Majalisar ta buƙaci hakan ne biyo bayan ƙudurin gaggawa da wakilin ƙaramar hukumar Birni da kewaye Alhaji Sarki Aliyu Daneji ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya nemi gwamnatin data tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa domin rage musu raɗaɗin iftila’in.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin da ta ɗaga darajar asibitin garin Gano, zuwa matakin babban asibiti domin ƙara inganta kiwon lafiya a yankin har ma da sauran yankuna, kamar yadda ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Shu’aibu Rabi’u ya buƙata.

Wakilinmu na majalisar Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a dai zaman na yau Laraba, shi ma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙaraye, Injiniya Ahmed Ibrahim, ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Kano ta gina titi a hanyar da ta tashi daga mahaɗar titin zuwa sansanin horas da matasa ƴan hidimar ƙasa, ta bi ta Kurugu da Dederi har zuwa Yammedi duk a yankin ƙaramar hukumar Ƙaraye.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sauya shugaban hukumar tattara haraji na jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Dakta Zaid Abubakar, a matsayin sabon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano, da kuma Kasim Ibrahim a matsayin babban daraktan hukumar.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da aka aikowa Dala FM Kano, a daren jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, tsohon shugaban hukumar Alhaji Sani Abdulkadir Dambo, an mayar da shi ne a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari, wanda kuma sauye-sauyen za su fara aiki nan take.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur: Fadar shugaban ƙasa kiyi wani abu dan mutane su samu sauƙi – Ƙungiyar Nothern Concern Soliderity

Published

on

Yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a ƙasar nan, ƙungiyar da ta damu da abubuwan da suka shafi arewacin ƙasar nan ta Northern Concern Soliderity, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi abinda ya dace dan ganin mutane sun samu wani sauƙi.

Babban jami’in gudanarwar ƙungiyar, kuma sakataren riƙo na zauren gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, Kwamared Saddat Usman Maiyaƙi, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, lokacin da yake nuna takaici kan irin wahalar da al’ummar ƙasa suke sha wajen shan man Fetur a gidajen man.

Ya ce duba da halin matsin rayuwar da al’umma suka samu kansu a ciki, akwai buƙatar shugabanni da masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen wahalar man Fetur ɗin da aka fama da ita.

Kwamared Saddat Maiyaƙi, ya kuma haƙurƙurtar da al’ummar ƙasar nan kan halin ƙuncin rayuwar da suka samu kai a ciki, inda ya yi fatan komai ya zo karshe cikin ƙanƙanen lokaci.

Continue Reading

Trending