Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya rantsar da sabbin Alƙalai a jihar

Published

on

Yanzu haka gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya rantsar da sabbin Alƙalai a matakan kotunan daban-daban na jihar ta Kano.

Hakan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Juma’a, da aka aikewa manema labarai.

Sanarwar ta ce Alƙalan da Gwamnan Kano ya rantsar sun haɗar da Alƙalan Babbar kotun Jiha guda tara (9), da kuma Alƙalan kotun ɗaukaka ƙara na shari’ar Musulunci guda uku (4), bayan da hukumar kula da sharia ta kasa (NJC) da kuma majalisar dokokin jihar Kano suka amince da naɗin nasu.

Haka kuma waɗanda aka naɗa a matsayin alƙalan babbar kotunan Jihar sune, Justice Fatima Adamu, Justice Musa Ahmad, Justice Hauwa Lawan, da Justice Farida Rabi’u Dan Baffa, da kuma Justice Musa Dahiru Muhammad.

Sannan kuma sauran su ne Justice Halima Aliyu Nasir, Justice Aisha Mahmud, Justice Adam Abdullahi, da kuma Justice Hanif Sunusi Yusuf.

A ɓangare guda kuma Alƙalan kotunan ɗaukaka ƙara na shari’ar Musulunci da aka naɗa sun haɗar da Khadi Muhammad Adam Kademi, da Khadi Salisu Muhammad Isah, sai kuma Khadi Isah Idris Sa’id, da kuma Khadi Aliyu Muhammad Ƙani.

Yayin da yake jawabi ga Alƙalan a wajen bikin rantsuwar da aka gudanar a ɗakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce an yi naɗin ne a bisa cancanta, inda naɗin nasu ya zama shaida da ke nuna ƙwarewar su ta fuskar shari’a, dama jajircewarsu wajen tabbatar da adalci da kuma doka da oda.

Gwamnan Kano ya kuma ce, “Haƙƙin da kuke ɗauka yana da yawa, kuma tasirin hukuncin ku ya kai ko’ina; Wannan nauyi ne da ke buƙatar ba wai kawai ƙwarewar shari’a ba har ma da zurfin fahimta, tausayawa, da jajircewa wajen kiyaye muhimman ƙa’idoji waɗanda aka gina tsarin shari’ar mu a kansu, “in ji Abba Gida-gida”.

Gwamna Abba Kabir ya ci gaba da cewa tun da aka kafa gwamnatinsa ta amince da mafi yawan buƙatu daga bangaren shari’a da ke da alaka da ƙudirin gwamnatin sa na raba madafun iko da ‘yancin kan ɓangaren shari’a, kamar yadda jaridar GTR Hausa ta rawaito.

Daga bisani dai Abba Kabir ya kuma buƙaci Alƙalan da su yi aikin su cikin tsoron Allah, tausayawa da jajircewa wajen yin hidima tare da bayyana kyakykyawan fata a gare su dangane da Wannan sabon nauyi da ya hau wuyan su.

Rahotanni sun bayyana cewar bikin rantsuwar ya samu halartar babbar Alƙaliyar alkalan jihar Kano, Mai shari’a Dije Aboki, da kuma Grandi Khadi na Kano, Khadi Tijjani Yusuf Yakasai, da Alƙalai da sauran jiga-jigan dake fannin shari’a daga bangarori daban-daban na ciki da wajen jihar Kano.

Manyan Labarai

Zamu ƙone duk kayayyaki marasa inganci da muka kama da zarar an gama shari’u – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta ƙone dukkanin kayayyaki marasa inganci da ta kama, da zarar an kammala dukkanin shari’un da suke a gaban Kotu.

Kwamishinan ma’aikatar ciniki da masana’antu, Adamu Aliyu Kibiya, ne ya tabbatar da hakan, a yayin wata ziyara ta musamman da ya kai hukumar kula da ingancin kayayyaki ta jihar Kano, a yammacin yau Alhamis.

Amadadin Kwamishinan babban sakataren ma’aikatar, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, da zarar an kammala Shari’un da masu kayan za’a ƙone su baki ɗaya.

“A bisa al’adar ma’aikatar ciniki da masana’antu, dama duk sabon Kwamishina idan ya zo yana ziyarartar hukumomin da suke da jiɓi da ma’aikatar domin duba irin aikace-aikacen su da sauran abinda ba’a rasa ba, hakan ya sa ma Kwamishinan ya ziyarci hukumar a yau, “in ji Ɗan-duwa”.

 

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, babban sakataren ya ƙara da cewa, ziyarar da Kwamishinan ciniki da masana’antun Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kai hukumar kula da ingancin kayayyakin, itace ta farko.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Trending