Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya gwangwaje ma’aikatan gidan gwamnatin jihar da kayan abinci da kuɗaɗe

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukan alheri ga ma’aikatan musamman idan suka tsaya tsayin daka a kan ayyukan su na dai-dai.

Injiniya Abba Kabir ya bayyana hakan ne yayin bayar da tallafin kayan abinci na miliyoyin Naira ga ma’aikatan gidan gwamnatin da su ke aiki tare da shi, a wani ɓangare na watan Ramadan mai alfarma.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun babban daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a jiya Lahadi, jim kaɗan da bayar da tallafin kayan abincin.

Daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin abincin sun haɗar da ma’aikata daga matakin aiki na 1 zuwa na 12, haka kuma kayan da aka basu sun haɗar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, da katon macaroni, sai buhun gero mai kwano 10, da kuma kudi N10,000 kowannen su.

Yayin da yake gabatar da kayayyakin cikin yanayi na musamman, gwamnan ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya ba shi damar yin hakan da nufin ganin an samu nasara ga ma’aikatan sa a cikin watan Ramadan mai albarka.

A cewar sa, “Yau rana ce ta Musamman a gare ni har ma’aikata na a gidan gwamnati domin na fara cika alkawuran yakin neman zabe da na inganta ayyukan jin dadi ga ma’aikatan gwamnati.” in ji gwamnan”.

Gwamnan Abba Kabir ya ƙara da cewa, dangantakar sa da ma’aikatan ba ta iya siyasa ba ce, a dan haka za su iya yin ra’ayoyin su daban-daban, amma abin da yake buƙata daga gare su shi ne sadaukarwa, aiki tukuru, da addu’a domin su cimma abin da suke yi a fagen aiki.

Daga nan sai ya yi kira gare su da su yi amfani da watan Ramadan ta hanyar yawaita ayyukan ibada tare da yin addu’a ga gwamnati da kasa baki daya Allah ya kawo mana dauki, musamman a wannan lokaci na matsin rayuwa.

Da yake jawabi tun da farko mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yabawa gwamnan bisa wannan karamcin da ya nuna, inda ya bayyana hakan a matsayin irinsa da aka taba samu a jihar.

Har ila yau, Kwamared Abdussalam ya yi kira ga waɗanda suka ci gajiyar shirin rabon kayan abincin da su mayar da hankali wajen sadaukar da ayyukansu, tare da rikon amana, da addu’a ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, domin ci gaba da samar da ayyukan alheri ga al’ummar jihar.

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Trending