Manyan Labarai
Al’adar Tashe: Ba za mu saurarawa masu ƙwacen waya da faɗan Daba ba – Ƴan Sandan Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ba za ta saurarawa dukkan irin matasan da suke ɗauke da ɗabi’ar nan ta ƙwacen wayoyin mutane, da faɗan Daba, da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ba, yayin gudanar da Al’adar Tashe a sassan jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan ta Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, da yammacin yau Laraba.
SP Kiyawa, ya kuma ce a ƙokarin su na samar da tsaro ga al’ummar Kano ne ma, Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel, ya yi zama da jagoran al’adar Tashen Auwalu Sani Sarki Na Lako, da masu ruwa da tsaki a harkar Tashen, domin zama na musamman dan nemo hanyoyin magance matsalar tsaro yayin Tashen a jihar.
“Kwamishinan ƴan sandan Kano SP Gumel ya baiwa baturen ƴan sanda da suke aiki a jihar Kano, da dakarun ƴan sandan, umarnin da su tabbata an bada tsaro a guraren da ake yin Ibada, “in ji SP Kiyawa”.
Rundunar ƴan sandan ta kuma umarci jami’an ts da su yi duk mai yiyuwa wajen hana masu ɗabi’ar ƙwacen wayoyin mutanen, da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, da magance faɗan Daba, yayin fitowa yin tashen a faɗin jihar Kano.
A al’adar Hausawa dai, an saba gudanar da tashen ne daga goma ga Azumin watan Ramadan, duk kuwa da wasu suna ganin cewar yanzu lamarin tashen ya juya inda wasu matasa suka mayar da Al’adar tashen zuwa yin abinda bai da ce ba, lamarin da ya sa ba’a fiya gudanarwa ba kamar baya.

Manyan Labarai
Ma’aikatan wutar lantarki za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Kano

Ƙungiyar ma’aikatan kamfanin samar da wutar lantarki ta ƙasa, za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a jihar Kano, daga gobe Laraba 21 ga watan Mayun 2025.
Sakataren tsare-tsare mai kula shiyyar Arewa maso yammacin ƙasar nan, na ƙungiyar Kwamared Muhammad Babangida, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren Talatar nan 20 ga watan Mayun 2025.
Ya ce sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon yadda suke zargin kamfanin KEDCO,.shiyyar jihar Kano, da gaza bai wa ma’aikatan kuɗin Fanshonsu aƙalla na watanni Ɗari da suka gabata.
“Yau kimanin watanni Ɗari ke nan, za a ciri kuɗin ma’aikata daga cikin albashin su a matsayin za’a kai kuɗin a hukumar Fansho, mun lura cewar kamfanin KEDCO, ba ya kai kuɗin inda ya dace don haka ne ma ba a biyan ma’aikata haƙƙin nasu, duk da da shi Ma’aikaci zai dogara da kan sa idan ya gama aiki, “in ji shi”.
Kwamared Muhammad, ya kuma ce sun yi bakin ƙoƙarin su don ganin an biya ma’aikata haƙƙin nasu ma watanni ɗari, amma hakan ba ta samu ba, a don haka ne suka ɗauki gaɓarar tafiya yajin aikin.
Ya kuma buƙaci al’umma da su yi haƙuri idan suka samu kan su a cikin Duhu, biyo bayan tafiya yajin aikin na sai baba ta gani da za su shiga, wanda suma ba a son ran su za su tafi ba sai don ya zama dole, domin neman haƙƙin su.
Sai dai har kawo yanzu kamfanin rarraba wutar lantarki KEDCO, bai yi komai ba akan batun, kuma mun yi ƙokarin jin ta ɓangaren mai magana da yawun kamfanin a Kano Sani Bala Sani, sai dai haƙan mu ba ta cim ma ruwa ba.

Manyan Labarai
Gwamnatin Kano ta dakatar da sanya tallace-tallacen maganin gargajiya a cikin fina-finai

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da sanya duk wani nau’in tallace-tallacen maganin gargajiya a cikin fina-finai ko masu yawo a tituna da lasifika, a faɗin jihar.
Shugaban hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano Abba Al-mustapha, ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Talata.
A cikin wata sanawa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a ranar Talata 20 ga watan Mayun 2025, ya ce an ɗauki matakin ne a wani ɓangare na tabbatar da bin ka’idoji da inganta sana’ar masu sayar da maganin gargajiya a Kano tare da masana’antar Kannywood.
Kazalika, shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce yawancin tallace-tallacen da ake yi a tituna da lasifika ko kuma a cikin Fina-finan na karya dokokin Hukumar, wadanda ke bukatar a tace su kafin a fitar da su ga jama’a.
“Muna umartar duk masu tallan maganin gargajiya a tituna da lasifika da sanyawa a cikin fina-finai da su miƙo tsarin tallace tallacen maganinsu, domin tantancewa tare da samun sahalewar Hukumar a cikin mako daya, tun daga ranar Laraba 21 ga watan mayun 2025, domin kaucewa daukar matakin doka, “in ji shi”.
Shugaban hukumar tace Fina-finan Hausa da Ɗab’i, ta jihar Kano, El-Mustapha, ya kuma yi kira ga dukkanin tashoshin talabijin tare da Hukumar Kula da kafafen yada Labarai ta Kasa (NBC) da su goyi bayan kokarin da hukumar ke yi.
Ya ci gaba da cewa, hakan ka iya tabbatar da ana bin dokar Hukumar, domin inganta tarbiyya a tsakanin al’ummar jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Manyan Labarai
Matashi ya gurfana a kotu da tuhume-tuhume goma sha ɗaya

Kotun majistrate mai lambar 23 ƙarkashin mai Shari’a Hajara Safiyyo Hamza, ta aike da wani matashi mai suna Mustapha Auwal Ɗan Hajiya, gidan ajiya da gyaran hali, bayan da aka gurfanar da shi da takardun tuhuma guda 11, masu ɗauke da laifuka daban-daban.
Tunda fari dai rundunar Ƴan Sanda ne suka gurfanar da matashin a gaban kotun, da zarge-zarge daban-daban, kuma cikin ƙunshin tuhumar har da zargin matashin da laifin Fashi da Makami guda biyar, yayin da sauran laifuka shidan kuma suka haɗar da haura gida da Sata.
Matashin dai an yi zargin ya jima yana addabar Al’ummar unguwar Bajanlaɓe da kewaye, inda a wannan karon aka samu nasarar kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotun.
Bayan da aka karanta wa Mustapha Ɗan Hajiya, ƙunshin tuhume-tuhumen ya musanta, sai dai ya amsa cewa mugun makamin da aka gabatar nasa ne, inda magatakardar kotun Muhammad Asharab Abdullahi, ya cike masa takardar zaman gidan ajiya da gyaran hali.
Kotun ta sanya ranar 21 ga watan yulin shekarar 2025, don a dawo da shi a ci gaba da sauraron tuhumar sa kan zargi guda shida na haura gida da sata wadanda kotun ta ke da hurumi akan su.
Wakilin Dala FM Kano, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki, ya ruwaito cewa, sauran tuhume-tuhumen guda biyar na fashi da makami kuma, kotun ta buƙaci a jira shawarar lauyoyin gwamnati, kasancewar kotun bata da hurumi kamar yadda lauyan gwamnati barista Ahamad Sarki ya roki kotun inda ta kuma amince da hakan.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su