Connect with us

Manyan Labarai

Cutar tarin Fuka na ƙara yaɗuwa cikin al’umma a Kano – Ma’aikatar lafiya

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce cutar tarin fuka na ƙara yaɗuwa a tsakanin al’umma, wanda hakan tasa gwamnati jihar ta samar da wajan gwaji a kananan hukumomi 44, dake Jiha.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar yaƙi da cutar tarin Fuka, da ya gudana a yau Asabar, wanda ma’aikatar lafiya ta shirya da haɗin gwiwar kungiyar Breakthrough Action.

Dakta Labaran ya ce a shekarar 2022, akwai mutane aƙalla Biliyan 10 da dubu Ɗari uku, wanda a shekarar 2023, mutane masu ɗauke da cutar tarin futar sun ƙaru zuwa miliyan 10 da dubu Ɗari Shida, wanda hakan ne ya bayar da tabbacin cutar na ƙara ta’azzara a cikin al’umma.

“Yanzu haka Najeriya, na mataki na shida a faɗin Duniya na yawan masu cutar tarin Fuka yayin da take mataki na daya a nahiyar Afrika, kuma jihar Kano na da tarin masu cutar, “in ji Kwamishinan”.

A cewar Abubakar Labaran, a shekarar da ta gabata kimanin mutane dubu Talatin da Tara da Ɗari Hudu da ashirin, aka tabbatar suna ɗauke da cutar a jihar Kano, wanda aka samu nasarar yiwa mutan Dubu Talatin da Shida da Dari Takwas da arba’in da Uku maganin cutar.

Ya ci gaba da cewa, “Daga cikin alamomin da ake gane mutum ya kamu da cutar tarin fukar akwai yin Tari Sama da Sati Uku, da zazzaɓi cikin Dare, da kuma yawan yin Gumi da sauransu, “in ji shi”.

Wakiliyrmu A’isha Shehu Kabara ta rawaito cewa, a nasa ɓangaren wanda ke kula ƙungiyar da aka yi haɗin gwiwar da ita wajen haɗa taron, ta Breakthrough Action, Ahmed Mu’azu, kira ya yi ga al’umma cewar, da zarar sun lura da guda daga cikin alamomin da Kwamishinan ya lissafa na kamuwa da cutar, ayi saurin zuwa Asibiti domin sai an gwada za’a tabbatar da halin da mutum ke ciki dan bashi agajin gaggawa.

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending