Connect with us

Manta Sabo

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, ta tabbatar wa iyalan Sharu Ilu Rami a Kano

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a sakatariyar Audu Baƙo a jihar Kano, ta yi hukunci akan shari’ar da dattijon nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata ya ɗaukaka, akan wani babban rami da aka yi taƙaddama akansa da ke unguwar Gwammaja a jihar.

Tunda fari dai dattijon ya ɗaukaka ƙarar ne akan hukuncin da babbar kotun kotun jaha ƙarkashin mai Shari’a Justice Usman Na Abba, ta yi, inda ta mallaka wa iyalan marigayi Sharu Ilu ramin, lamarin da dattijon ya ɗaukaka ƙarar.

Sai dai kuma a zaman kotun na yau Laraba, alkalin da ya jagoranci yanke hukuncin a kotun ɗaukaka ƙarar Justice U-A Musalli, ya kori ƙarar dattijon, tare kuma da tabbatar da hukuncin kotun ƙasa, ma’ana dai a baiwa magada iyalan marigayi Sharu Ilu ramin kamar yadda aka yi hukuncin baya a kotun ƙasan.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u, ya yi duk mai yiyuwa dan ji daga ɓangaren lauyar Dattijo Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, mai suna Veronika, sai dai ta ce ba abinda za ta ce, a nan ne ya wai-wayi guda daga cikin lauyoyin waɗanda akayi ƙara mai suna Yahya Y Sharif, wanda ya ce daman haka suka yi tsammani, kuma gashi gaskiya tayi halin ta.

Daga bisani dai kotun ta ce a shirye take da ta baiwa kowanne bangare kwafin hukuncin, kuma duk wanda bai gamsu da hukuncin ba yana da dama ya wuce kotun gaba.

Aƙalla dai an shafe sama da shekaru biyar ana taƙaddamar ramin dake unguwar Gwammaja a Kano.

Manta Sabo

Kotu ta hana duk wata kafar yada labarai yin labarin da ya shafi Auwalu Danladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 4 karkashin jagorancin mai Shari’a Usman Na Abba ta yi hani ga duk wasu Jami’an Ƴan sanda ko na duk wata hukuma ta daban daga gayyata ko tsangwama, ko kuma bincike ko kamawa, ta kowace siga ga kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa Auwalu Ɗanladi Sankara.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kotu ta wanke Auwalu Sankara daga zargin mu’amala ko alaƙa da juna tsakanin mai ƙara da Taslim Baba Nabegu har zuwa lokacin sauraran ƙarar.

Kotun ta kuma amince da rokon da wani lauya mai suna Barrister I.C Ekpinovi ya yi amadadin mai kara Auwalu Danladi Sankara wanda ya yi karar Nasiru Buba.

Mai karar ta bakin lauyansa ya bayyana wa kotun rokonsa inda ya roki kotun da ta dakatar da wanda ake kara ko dai shi da kansa ko kuma ƴan korensa daga ci gaba da yaɗa wata magana wadda wata babbar kotun Shari’ar Muslunci da ke Kano ta rufe.

Mai Shari’a Usman Na Abba ya ayyana cewar ko dai wanda aka yi kara ko yan korensa ko kuma wasu wakilansa, da a dai na yaɗa waccan magana har zuwa lokacin da kotun za ta saurari kowanne ɓangare.

Kotun ta ayyana cewar ta yi hani ga duk wata kafa ta yada labarai ko dai Rediyo ko Talabijin, ko shafukan sada zumunta da kafar Intanet da duk wata kafa wadda take iya sadar da labarai, daga yaɗa labaran da suka shafi Auwalu Ɗanladi Sankara da Taslim Baba Nabegu.

A ranar Talata ne dai gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya bayyana mayar da Auwalu Ɗanladi Sankara muƙamin sa na Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar, bayan da kotu ta wanke shi daga zargin da hukumar Hisbah ta Kano, ta yi masa kan zargin baɗala da wata matar aure.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa kotun ta kuma sanya ranar 28 ga wannan watan na Nuwamba dan sauraron kowane ɓangare akan shari’ar.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta dakatar da rantsar da Ali Musa Wardwoker ko Ghali Basaf a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso

Published

on

Babbar Kotun jaha mai lamba huɗu da ke zamanta a sakateriyar Audu Bako a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Usman Na’abba, ta bayyana matsayarta akan hukuncin da ta yanke dangane da shari’ar da ake yi a tsakanin Ali Musa Hardworker da Jam’iyyar NNPP a Kano.

Kotun ta ayyana cewar kowanne ɓangare ya dakata da batun rantsuwar kama aiki har zuwa lọkacin da kotun ɗaukaka ƙara za ta ayyana matsayarta.

Idan dai ba’a manta ba Dala FM ta ruwaito yadda a baya kotun ta ayyana Ali Musa Hardworker a matsayin halastaccen ɗan takarar lamarin da ya sanya jam’iyyar NNPP da Ghali Basaf suka ɗaukaka ƙara akai.

Continue Reading

Manta Sabo

An zargi wani Matashi da satar wayar direban mai Shari’a ana tsaka da Shari’a a Kano

Published

on

Babbar Kotun jaha mai zamanta a miller road karkashin jagorancin mai Shari’a Maryam Ahmad Sabo, ta yi umarnin yan sanda su fadada bincike akan wani matashi mai suna Haruna Buhari wanda ake zargi da laifin kutse da sata.

Tunda fari dai an zargi Haruna da kutsawa cikin ofishin mai Shari’ar tare da ɗauke wayar salula ta direban mai shari’ar wadda aka jona caji a ofishin ta.

Tuni dai yan sandan kotun suka fice da shi daga Harabar kotun dan mika shi shelkwatarsu da ke Bompai, domin gudanar da binciken.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da wani shaidar gani da ido wanda yace daman an dame su da satar takalma a masallacin harabar kotun idan sun je Sallah, a Masallaci.

Mai korafin dai ya kuma bayyana cewar an fi satar takalman alkalai a masallacin.

Continue Reading

Trending