Connect with us

Manta Sabo

Kotu ta gindaya sharuɗa ga ƴan Daudun da ake zargin kai wa ofishin Hisbah Hari kafin bada berlin su a Kano.

Published

on

Babbar kotun shari’ar Muslunci da ke zamanta a Shahuci, karkashin jagorancin mai Shari’a Muhammad Sani, ta bayar da belin matasannan da ake zargin sun farfasa motar hukumar Hisba, tare da yunkurin ƙona ofishin hukumar na Bachirawa karshen kwalta da ke Kano.

Tun da farko, ƴan sanda ne suka yi zargin matasan da laifukan haɗa baki, da barnatar da kayan gwamnati, da kuma yunƙurin ƙone ofishin Hisbah.

Lamarin dai ya faru ne a unguwar Bachirawa titin jajira, inda ƴan kwamitin unguwar suka kama wasu karti suna zagaye gidan Tururuwa da talatainin dare, bayan an kama sune kuma waɗannan matasa da ake zargin ƴan Daudu ne suka kai wa ofishin Hisbar na yankin hari.

A yayin da yake bayyana matsayar kotun mai Shari’a Muhammad Sani, ya ayyana cewar kotun ta bayar da belin su, sai dai ya gindaya musu wasu sharuɗa.

Daga cikin sharuɗan, kotun ta ayyana cewar sai an ajiye kaso daya bisa uku na abin da ake zargin sun lalata, idan kuma suka tsere mai karbar belin zai biya dubu dari biyu akan kowane mutum daya, an kuma ayyana cewar ɗan uwa na jini shine kawai yake da ikon karƙar belin idan kuma sun sake aikata wani laifin to belin ya karye.

Kotun ta sanya ranar 22 da 23 ga watan gobe dan fara sauraron shaidu.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar matasan sun hadar da Nasiru Hamisu Na kabara, da Auwal Haruna da kuma mutum 3.

Manta Sabo

Wata Kotu a Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar da aka shigar da ƙaramar hukumar Gwale da wani mutum

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 15 da ke zamanta a Mila Road a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta ci gaba da saurarar karar da al’ummar unguwar Dorayi Baba unguwar jakada suka shigar da karamar hukumar Gwale, da wani mutun mai suna Alhaji Ibrahim Ƴan Shana.

Tunda fari dai mutanan unguwar sun shigar da karar ne suna zargin karamar hukumar ta Gwale, da cefanar wa Ibrahim ‘yan Shana wani fili mallakin al’ummar unguwar na makaranta, lamarin da su garzaya gaban kotun tun a shekarar 2023, a lokacin shugabancin ƙaramar hukumar da ya shuɗe, suna rokon da ta dawo musu da shi domin a gida makaranta a yankin nasu.

Sai dai a zaman kotun na yau bangaren wadanda ake kara na daya wato karamar hukumar Gwale sun gaza gabatar da martanin su akan karar, inda suka roki kotun da ta sanya wata ranar domin gabatar da martanin nasu.

Wakilimmu Mu’az Musa Ibrahim ya rawaito cewa mai shari’ar ya sanya ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2024 domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta aike da matashin da ake zargi da kashe matar sa gidan yari a Kano

Published

on

Kotun majistret mai lamba 29 karkashin jagorancin mai Shari’a Talatu Makama, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.

Matashin mai suna Adamu Ibrahim ana zargin sa ne da laifin hallaka mai ɗakinsa ta hanyar kwantara mata dutsen Guga, a fuskarta a can garin kwanar ɗan gora.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar, tun a ranar 9 ga watan 4, wani mai suna Idris Adamu yaje caji ofishin ƴan sanda inda ya shigar da kara akan cewar Adamu Ibrahim ya kashe mai ɗakinsa wadda kuma kanwa ce a wajen mai ƙarar Idris Adamu.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’ila, ya zanta wanda ake zargi wanda ya ce tsautsayinya sanya shi aikata hakan.

Shima dan uwan marigayiyar ya bayyana matsayarsu, inda ya roƙi kotun da ta yi musu adalci a shari’ar.

Kotun dai ta sanya ranar 17 ga watan gobe dan a kara gabatar da shi a gaban ta domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Trending