Manyan Labarai
Mutanen da suka rasu a haɗarin Tirela sun sake ƙaruwa zuwa 15 a Kano

Rahotanni daga garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano, na nuni da cewa zuwa yanzu aƙalla mutane 15, ne suka rasa ran su, sakamakon haɗarin motar Tirela da ya faru da su a ranar Juma’a 28 ga watan Yunin 2024.
Wani mazaunin garin ya shaidawa wakilin Dala FM Kano, Mu’azu Musa Ibrahim, cewa, a yau Asabar ne aka samu ƙarin mutum ɗaya da ya rasu, wanda hakan ya tasamma mutane 15, da suka rasa ran su.
Ya ci gaba da cewa, “An kuma sallamo mutane takwas daga asibiti, wasu daga cikin su na ɗauke da Karaya biyu zuwa uku an ɗora su, wasu kuma ɗauke da raunuka daban-daban a sassan jikin su, “in ji shi”.
A ranar Juma’a ne dai aka samu Ifrila’in hadarin wanda babbar motar Tirelar ta suɓucewa Direbanta, inda tayi kan masallata da suke ƙokarin komawa Gida da guraren kasuwancin su, jim kaɗan bayan idar da sallar juma’a, a garin na Imawa, lamarin da zuwa yanzu ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 15, wasu kuma suke kwance a Asibiti.
Bayan kuma faruwar al’amarin al’ummar garin suka kulle titin da ya taso daga Zaria zuwa Kano, tare da gindaya sharaɗin cewar ba za su buɗe hanyar ba sai an kammala jana’izar mamatan, sai dai kuma a maƙabarta ne manyan gari suka bai wa mutane hakuri, tare da shawo kan su, inda suka buɗe hanyar aka fara wuce tun a jiyan.

Manyan Labarai
An yi jana’izar Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ahmadu Haruna Zago

Ɗaruruwan mutane ne suka halarci sallar jana’izar shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna zago, wanda aka gudanar a kofar kudu a fadar mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu.
Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shine ya jagorancin sallar jana’izar a tsakar ranar Alhamis ɗin nan.
Daga cikin manyan manyan mutane da Suka hallarci sallar jana’izar marigayin Alhaji Ahmadu Haruna zago, akwai gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da tsohon kwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso, da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, da sauran manyan mutane ciki har da masu riki da mukaman gwamiti.
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne dai marigayi Ahmadu Zago, mai shekaru 74 ya rasu, a Asibitin Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya, kafin rasuwar sa yana da mata huɗu da ƴaƴa 37, da jikoki da dama.
Mai martaba sarkin kano Khalifa Muhammadu Sunusi na yayi addu’ar fatan Allah ya jikan marigayin ya kuma baiwa iyalansa da al’ummar jihar Kano jure rashin.
Tuni dai gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga al’ummar jihar da kuma iyalan marigayi Ahmadu Haruna Zago, tare da fatan Allah ya gafarta masa.

Manyan Labarai
Majalisar dokokin Kano ta amince da kafa rundunar tsaro mallakin jihar

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa Rundunar tsaro mallakin gwamnatin jiha, bayan ɗaukar tsawon lokaci ana dambarwa a majalisar kan saɗarar dokar da ya ce ba’a yarda wanda yake riƙe da katin shaidar kowace jam’iyyar siyasa ba ya shugabanci rundunar tsaron.
Majalisar ta amince da samar da dokar ne bayan shafe kusan fiye da tsawon awa ɗaya ana muhawara akan da yawa daga cikin tanadin da dokar samar da rundunar tsaron ya yi kafin ayi mata karatu na uku.
Da yake ƙarin bayani akan kunshin dokar, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Husani Dala, ya ce sun yi cikakken Nazari da hangen nesa kafin yin dokar wadda zata taba kowane bangare na jihar Kano wajen daukar ma’aikatan ta musamman wadanda basu da alaka da harkar siyasa.
“Dokar da muka samar ta amincewa jami’an rundunar tsaron ta jihar Kano da za a kafa su ɗauki kowane irin makami domin gudanar da ayyukan su, wanda ya haɗa da kamawa, hana aikata laifi da fatattakar masu aikata laifuka a fadin jihar Kano, “in ji Dala”.
Ditective Auwal Bala Durumin Iya guda daga cikin masana harkokin tsaro ne a ƙasar nan, ya ce akwai buƙatar abi ƙa’idoji wajen ɗaukar jami’an da za su gudanar da aikin rundunar tsaron da zarar gwamnan Kano ya sanya hannu a kan dokar.
A dai zaman na ranar Talata 04 ga watan Fabrairun 2025, majalisar dokokin Kano ta kuma amince da yin gyara akan dokar hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan, da hukumar da ke kula da sufuri a kwaryar birnin kano domin samun damar nada musu mataimaka.

Manyan Labarai
Za’a fara cin tarar Naira dubu 25 akan masu tofar da Yawu ko Majina, ko zubar da Shara ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar cin tarar Naira dubu 25 ga duk wanda aka kama da tofar da Yawu, da Majina, yin Bahaya ko zubar da Shara a sha tale-tale da kuma karkashin gadojin dake Kano.
Wannan ya biyo bayan dokar da majalisar ta Samar wadda za ta gudanar da ayyukan hukumar ƙawata birnin Kano da Kula da wuraren shaƙatawa.
Da yake Karin bayani ga manema labarai, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala, ya ce ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan da za su tsaftace Kano domin shigar da jihar sahun biranen duniya a fannin tsafta da cigaba.
“Bayan tarar ta Naira dubu 25, akwai kuma sauran hukunce-hukunce da dokar ta tanada wadanda za’ayi amfani dasu wajen ladabtar da duk wanda aka samu da laifukan, “in ji Lawan Dala”.
Majalisar ta kuma yi karatu na biyu kan gyaran dokar hukumar kwashe Shara da tsaftar Muhalli ta Kano domin Samar da mataimakin Shugaba.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su