Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta tallafawa iyalan mutanen da haɗarin Tirela ya rutsa da su har wasu suka rasu a Kura

Published

on

Yayin da ake ci gaba da jimamin asarar rayukan da haɗarin wata babar motar Tirela ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 15, bayan da ta danne masallata da dama a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura a ranar juma’ar da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta tallafawa iyalan wadanda hadarin ya rutsa dasu.

Gwamnan jihar kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya buƙaci matuƙa ababen hawa da su ƙauracewa gudun wuce kima musamman ma a lokacin da suke gab da shigowa cikin gari, domin kare al’umma daga iftila’in hatsari, kamar yadda aka samu asarar rayuka a wannan yankin.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne yayi wannan jawabin ne da yammacin jiya, yayin da ya kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga al’ummar yankin da wannan iftila’in haɗarin Tirelar ya faru da su.

“Gwamnatin mu za ta tabbatar da cewa an tallafawa dukkannin iyalan da waɗanda iftila’in ya afkawa domin rage musu wani raɗaɗin halin da suka samu kan su a ciki, “in ji Abba Kabir”.

Gwamnan ya kuma bada umarnin waɗanda suke a asibitin garin Kura, da a mayar dasu babban Asibitin birni, domin ci gaba da kulawa da lafiyar su.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnatin Kano ta bayar da kuɗi Naira dubu ɗari biyar ga kowanne iyalan mamatan, domin yin addu’a garesu.

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta ɗage komawar ɗalibai makarantu Firamare da na Sakandire

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ɗage komawa makarantun Firamare da na Sakandire daga ranar Lahadi da Litinin, har zuwa wani lokaci da za a saka a nan gaba.

Kwamishinan Ilmi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren yau Asabar 07 ga watan Satumban 2024.

Doguwa ya kuma ce gwamnatin ta yi niyyar buɗe makarantun kwana ne daga gobe Lahadi, yayin da na jeka ka dawo kuma ana kuɗiri aniyar buɗewa daga ranar Litinin, amma sakamakon wani abu na gaggawa da ya taso ya sanya aka ɗage komawa makarantun zuwa wani lokaci da za’a saka a nan gaba.

Kwamishinan Ilmin ya kuma bai wa iyayen yara haƙuri bisa jinkirin komawa makarantar da aka samu, wanda ya ce an yi hakan ne domin cikar daraja da mutumtakar ƴaƴan su, da kuma ƙara shiri akai.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun cafke yaron da suke satar Adai-dai ta sahu da wasu matasa a Kano – Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snaching

Published

on

Rundunar tsaro da ke yaƙi da ƙwacen waya da faɗan Daba da kawar da Shaye-shaye ta Anti-Phone Snaching da ke jihar Kano, ta samu nasarar cafke wani Yaro da bai wuce shekaru 14 ba, da ake zargin wasu matasa sun haɗa kai da shi suka saci wani baburin Adai-dai ta sahu a unguwar Gammaja Tagwayen Gida.

Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-Phone Snaching, Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyanawa Dala FM Kano a ranar Juma’a, ya ce sun cafke matashin da baburin ne a cikin tsakar daren Laraba da misalin ƙarfe 04:00, a lokacin da suke sintiri, inda suka ci karo da matasan.

“A lokacin da muka yi kan matasan su huɗu da suke cikin baburin Adai-dai ta sahun inda uku suka tsere muka samu nasarar cafke Yaron ɗan unguwar Ɗorayi da Babur ɗin, amma muna ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin kamo sauran matasan, “in ji Inuwa Sharaɗa”.

Kwamandan rundunar ya kuma ce a lokacin da suka cafke yaron ana tsaka da ruwan sama ne har ma ruwan ya jiƙa su sosai bisa rashin rigar ruwa da suke fama dashi, tare da fuskantar ƙarancin kayan aiki, har ma guda cikin ma’aikatan su ya faɗi tare da jin ciwo.

Hamisu Ahmad, shine Ma-mallakin Babur ɗin, ya ce a lokacin da aka sace masa baburin ya matuƙar shiga cikin damuwa duk da dai satar Babur ɗin shine karo na biyu.

Yaron da rundunar ta kama ya shaidawa Dala FM Kano cewa, su huɗu ne suke fita satar baburin Adai-dai Sahun, da kuma satar wayoyin mutane idan an ɗauka su sayar, amma ya yi nadama idan aka sake shi zai koma makaranta duk da mahaifin sa ya kareshi daga gidan su.

A cewar sa, “Mahaifina ya koreni nida ƙanena saboda yadda muke ƙin zuwa makaranta, amma dai idan na fita zan koma in bashi haƙuri domin nima abin ya dameni, “in ji yaron”.

Mai baburin ya kuma miƙa godiyar sa ga Allah S.W.T. tare da godewa jami’an rundunar bisa nasarar da aka na ganin Babur ɗin nasa har ma aka kama yaron da ake zargin sun sace ɗan sahun.

Majiyar Dala FM Kano, ta rawaito cewa, Inuwa Salisu Sharaɗa ya ƙara da cewa za su zurfafa bincike akan al’amarin gabanin bai wa wanda ya zo ya ce babur ɗin nasa ne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Ruguzowar Gini ya yi sanadiyyar rasuwar mutane uku da jikkatar wasu a Kano

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane uku a unguwar Sabon gari yankin Noman’sland da ke ƙaramar hukumar Fagge a Kano, sakamakon yadda gidan da suke mai hawa biyu ya ruguzo musu su biyar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar PFS Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyanawa Dala FM Kano, hakan a ranar Alhamis, ya ce iftila’in ruguzowar ginin ya rutsa da mutane biyar biyo bayan mamakon ruwan saman da akayi a daren jiya Laraba.

Ya ce bayan da aka kai su Asibiti ne likitoci suka tabbatar da rasuwar mutane uku yayin da biyu suke karɓar kulawar likitoci.

Saminu Yusif ya kuma tabbatar da ruguzowar wani gini mai hawa ɗaya a unguwar Sharaɗa Turba layin Service da ke ƙaramar hukumar Birni, da ya faɗawa mutanen gidan su shida, inda jami’ansu suka kai su Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, yayin da suke karɓar kulawar likitoci.

A cewar sa, “Mun kuma samu labarin yadda wani gini mai hawa ɗaya da gaban gidan ta ruftawa mutane uku a unguwar Ƙofar Nassarawa Movie Quarters, daga bisani jami’an mu suka kai ɗauki, “in ji Samun Yusif”.

SC Musbahu ya ƙara da cewa, hukumar ta samu kiran gaggawa ne akan iftila’in ruftawar gine-ginen a ranar Alhamis, daga ɓangarorin da al’amarin ya faru, inda jami’ansu suka kai ɗaukin gaggawa.

Continue Reading

Trending