Connect with us

Labarai

Ƴan Majalisu, Malamai, da gwamnoni ya kamata ku faɗawa Tinubu gaskiya kan halin da Talakawa suke ciki – Human Right 

Published

on

Ƙungiyar kare hakƙin ɗan adam ta Sustainable Growth Initiatives for Human Right Development, ta ce akwai buƙatar Sanatoci, da ƴan majalisar tarayya da kuma Malamai, su faɗawa shugaban ƙasa Bola Tinubu gaskiya wajen yin abinda ya dace kan tsadar rayuwar da al’umma suke ciki, biyo bayan janye tallafin man fetur, da kuma ƙarin farashin da suke samu.

Daraktan ƙungiyar a matakin ƙasa Kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ne ya bayyanawa Dala FM hakan, a wani ɓangare na nuna takaicin sa kan yadda daga lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗare karagar mulki kukan al’umma ya ƙara ninkuwa, al’amarin da ke damun su.

Kwamared Abubakar Musa ya ce yadda al’ummar ƙasa suke ci gaba da fuskantar halin tsadar rayuwa, kamata ya yi ta fito da sabbin tsare-tsaren da za su taimake su, ba wai yin abinda zai ci gaba da musguna musu ba.

A cewar sa, “Daga lokacin da kuɗin man fetur ya nunka to komai ma ninkawa yake yi wanda harkokin kasuwanci, da cin Abinci ga mutane, da sauran buƙatu duk suka ɗai-ɗai ce, a don haka ya kamata Sanatoci, da Ƴan Majalisar Wakilai, da gwamnoni, da dukkanin masu ruwa da tsaki ku yi abinda ya dace domin ganin al’umma sun samu sauƙi, “in ji shi”.

Kwamared Abubakar ya ƙara da cewar ya kamata suma malamai su tashi tsaye wajen faɗawa shugabanni gaskiya, wajen ganin sun tausayawa al’umma domin samun mafita daga acikin yanayin tsadar rayuwar da suke ciki a ƙasa.

Al’ummar ƙasar nan dai sun sake shiga cikin mawuyacin hali ne tun bayan da shugaba ƙasa Bola Tinubu ya ayyana janye tallafin man fetur, jim kaɗan da rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Yanzu haka dai mafi yawan gidajen man ƴan kasuwa a sassan jihar Kano, suna sayar da kowacce litar Fetur ɗaya akan kuɗi Naira 11,00, wasu kuma 1150, zuwa 1,200, yayin da na NNPCL ke sayar da kowacce lita ɗaya 10,30, a Arewa maso Yammacin Najeriya, abin da ke damun al’umma, ki da dai a wasu ɓangarorin ƙasar yake zarta hakan.

Baba Suda

Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Published

on

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.

Cikakken labarin na Zuwa….

Continue Reading

Baba Suda

Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.

Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.

 

Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

 

 

Continue Reading

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

Continue Reading

Trending